Atiku Ya Fara Fuskantar Matsala a ADC, Ana So Ya Canza Mataimakinsa a Zaben 2027

Atiku Ya Fara Fuskantar Matsala a ADC, Ana So Ya Canza Mataimakinsa a Zaben 2027

  • Wata kungiyar siyasa ta bukaci Atiku Abubakar ya sauya tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa
  • Kungiyar ta ce Amaechi ba shi da karfin siyasa da zai kara wa ADC damar samun kuri'u a babban zaben 2027 mai zuwa
  • Kungiyar SPPAF ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya zabi mataimaki mai farin jini da karfin goyon bayan jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wata kungiya mai suna Southern Political Progressives Amalgamation Forum (SPPAF) na son a cire tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi daga matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC.

Ta gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da kada ya tafi da tsohon gwamnan Jihar Rivers din a matsayin mataimakinsa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar yana jawabi a babban taron ADC na ƙasa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masu magana da yawun SPPAF, Johnson Iheanacho, Eniafe Ayomide da Anga Fidelis suka fitar ranar Juma'a.

Kungiyar ta ce hadakar jam'iyyun adawa a karkashin jam'iyyar ADC ta ba 'yan Najeriya fata na samun wata sahihiyar madadin jam'iyya mai mulki ta APC.

SPPAF ta yi fatali da zabar Amaechi

Kungiyar ta bayyana damuwa kan rahotannin da ke cewa Atiku ya amince da Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa.

Ta ce kalaman da Amaechi ya yi a lokacin zaben fidda gwani na jam'iyyar sun haifar da shakku kan yadda zai kasance mai cikakken biyayya ga hadakar.

A cewarta, Amaechi ya taba nuna shakku kan yiwuwar Atiku ya kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sannan ya yi watsi da batun cewa zai iya zama mataimakin Atiku.

Kungiyar ta ce:

"Labarin Atiku ya duki Amaechi a matsayin mataimakinsa abin damuwa ne. Tsohon ministan ba shi da irin karfin siyasar da zai jawo wa ADC karin kuri'u."

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

"Amaechi ba zai iya tabbatar wa jam'iyyar nasara a Jihar Rivers ko yankin Neja Delta baki daya ba, kuma zai zama nauyi maimakon amfani ga jam'iyyar."
Atiku da Amaechi.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar tare da mataimakinsa, Rotimi Amaechi Hoto: @Atiku
Source: Twitter

An ba Atiku shawara kan Amaechi

Kungiyar ta kuma yi ishara da wasu rahotanni da ke cewa Amaechi ya bukaci a ba shi ikon zabar masu rike da wasu manyan ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matsayin wani bangare na tattaunawar kujerar mataimakin shugaban kasa.

Sai dai ta amince cewa ba a tabbatar da sahihancin wadannan rahotanni ba, kamar yadda rahoton Daily Post ya nuna.

A karshe, kungiyar ta shawarci Atiku da ya zabi mataimakin da ke da karfin goyon bayan jama'a da kuma tasiri a siyasance.

Ta ce irin wannan mataki zai kara wa ADC damar kayar da jam'iyyar APC a babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Malami ya karbi bakuncin Amaechi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya gana da dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ganawa ta jiga-jigan biyu ta gudana ne ranar Juma'a, 3 g watan Yulin 2026 a gidan Malami da ke Abuja.

Ganawar ta zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan Amaechi ya kai ziyara ga tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262