Ana Neman Yi wa Gwamna Inuwa Karan Tsaye kan Ɗan Takarar Sanata a Gombe
- Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta fara sauraron ƙarar da ke neman a soke tikitin takarar Sanatan APC na Gombe ta Kudu
- Mai ƙarar ya ce babu zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a gundumomi 40 na mazaɓar, yana neman kotu ta umarci a sake gudanar da sahihin zaɓe
- Shaidu huɗu sun tabbatar da ikirarin mai ƙara, yayin da kotu ta ɗage shari'ar domin bai wa waɗanda ake ƙara damar gabatar da nasu shaidu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Kotun Tarayya da ke Gombe ta soma sauraron ƙarar da aka shigar da ɗan takarar sanata a jam'iyyar APC.
Wanda ya nemi takarar kujerar a APC, Bilyaminu Babadidi, shi ya shigar yana ƙalubalantar sahihancin tikitin takarar Sanata na jam'iyyar a mazaɓar Gombe ta Kudu.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya ce mai karar ya sanya sunan APC, Jerry Damara da kuma INEC cikin waɗanda ake ƙara.
Zargin da ake yi kan dan takarar sanatan
A cikin ƙarar, Babadidi ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani a kowace gunduma daga cikin gundumomi 40 da ke mazaɓar ba.
Ya ce duk da haka an ayyana Jerry Damara a matsayin ɗan takarar jam'iyyar ba tare da bin ƙa'idoji da tsarin APC ba.
Mai ƙarar ya bayyana cewa tun farko ya kai koke ga kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafen bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar, amma har zuwa yanzu ba a ba shi damar samun hukunci kan korafin ba.
Saboda haka, ya roƙi kotu ta soke amincewar da aka ba Jerry Damara a matsayin ɗan takarar Sanatan APC na Gombe ta Kudu.
Haka kuma ya nemi a ba da umarnin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani bisa tanadin doka.

Source: Original
Shaidar da wasu mazauna yankin suka bayar
Lauyan mai ƙarar, Barista Ayuba Rabiu, ya gabatar da shaidu huɗu tare da wasu takardu domin tabbatar da hujjojinsu.
Daga cikin shaidun akwai Musa Gebi, Emmanuel Abel Bable, Stash da kuma Bilyaminu Babadidi da kansa, cewar Daily Post.
Dukkan shaidun sun shaida wa kotu cewa babu wani zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a kowace gunduma cikin gundumomi 40 na mazaɓar Gombe ta Kudu, sun nace cewa abin da aka yi bai dace da tsarin zaɓen jam'iyyar ba.
Bayan sun kammala bayar da shaidarsu, lauyoyin APC, Jerry Damara da INEC sun yi musu tambayoyi domin gwada ingancin bayanansu a gaban kotun kafin a ci gaba da shari'ar.
Da aka kammala wannan mataki, lauyan mai ƙarar ya sanar da kotu cewa ɓangarensu ya rufe gabatar da shaidu, daga nan aka shirya ba wa ɓangaren waɗanda ake ƙara damar gabatar da hujjojinsu.
Sanata ya koma PDP bayan rasa tikitin APC
A wani labarin, an ji cewa wani sanata a Gombe ya jawo wa APC matsala bayan ta rasa daya daga cikin ƴan majalisa da take da su a Najeriya.
Sanata Anthony Siyako Yaro ya fice daga APC bayan gaza samun tikitin takara domin komawa kan kujerarsa a zaben 2027.
Ya sanar da sauya shekarsa zuwa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP wadda bai dade da ficewa daga cikinta ba.
Asali: Legit.ng


