Yadda Sojoji Suka Fatattaki 'Yan Ta'adda da Suka Kai Hari Sansanin Sojojin Zamfara
- Dakarun sojin Najeriya sun yi namijin kojari wajen tunkarar wasu masu dauke da makamai da ake zargin 'yan ta'adda ne bayan sun kai masu hari a Zamfara
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan masu tarin yawa sun kai harin amma an yi gaggawar tura wa sojojin karain dakaru daga sansanoni biyu
- Harin da aka kai sansanin sojoji na FOB wanda ke karamar hukumar Bukuyyum da ke jihar Zamfara da zummar jawo gagarumar asara ga jami'an tsaron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani yunkuri da ake zargin 'yan ta'adda ne suka yi na kutsa kai tare da kai hari kan wani Sansanin Sojin FOB da ke karamar hukumar Bukuyyum a jihar Zamfara.
Rahotannin sirri sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2.45 na rana a ranar Alhamis, 2 ga Yulin 2026, lokacin da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka yi kokarin kai hari kan dakarun da ke FOB Gwashi.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun ce dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa tare da amfani dagwada masu kwanji, lamarin da ya jawo kazamin artabu tsakanin bangarorin biyu.
Sojoji sun gwabza da yan ta'adda a Zamfara
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa sakamakon yadda sojojin suka yi fito-na-fito da maharan, 'yan ta'addan sun gaza cimma manufarsu, inda suka tsere daga yankin bayan sun yi watsi da harin.
Bayan dakile harin, rundunar soji ta tura karin dakaru daga sansanonin FOB da ke Gummi da Bukuyyum domin kara karfafa tsaro a yankin tare da tallafa wa ayyukan bincike da fatattakar maharan.
Majiyoyin sun ce dakarun sun kuma kara tsaurara sintiri da sa ido a yankunan da ke kewaye domin hana 'yan ta'addan sake haduwa ko kuma kaddamar da wani sabon hari.
Haka kuma, an kara inganta matakan kariya a sansanin domin tabbatar da cewa yankin ya ci gaba da kasancewa cikin tsaro.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Sojoji sun cafke jami'an tsaro da ke safarar makamai ga 'yan ta'adda
Babu asarar rayuka a bangaren sojoji
Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya samu raunuka yayin musayar wutar da aka yi da maharan.

Source: Twitter
A cewar majiyoyin, yadda dakarun suka mayar da martani cikin sauri ya nuna cikakken shirin da suke da shi na dakile duk wani yunkurin 'yan ta'adda na samun damar gudanar da hare-hare a yankunan da suke aiki.
Sun kara da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da sintiri da kuma ayyukan leken asiri domin bibiyar maharan da suka tsere tare da ci gaba da matsa wa kungiyoyin masu aikata laifuka a jihar Zamfara lamba.
Zamfara: An kama kaya irin na sojoji
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun kama wanda ake zargi da shirin kai wa 'yan ta'adda kaya don ba su damar ci gaba da kai harin ta'addanci a Zamfara.
Zamfara Sojojin Najeriya sun yi nasarar kwato takalma irin na sojoji guda 150 da wasu kayayyakin da dakaru ke aiki da su da kuma da na'urori a wajensu yayin da aka matsa wuta wajen kara zurfafa bincike.
Bayanai sun nuna cewa ana ci gaba da bincike game da mutanen, yayin da sojoji suka bukaci jama'a su rika bayar da sahihan bayanai ga jami'an tsaro a kan lokaci da zarar sun samu bayanan.
Asali: Legit.ng

