Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa

  • Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da ɗaya daga cikin yan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Wannan ne karon farko da Tinubu ya shiga ganawa da Kwankwaso tun bayan hawa gadon mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023
  • Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, yana cikin waɗanda suka gwabza da Bola Tinubu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023

FCT Abuja - Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa yanzu haka shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a Aso Rock, Abuja.

Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa na sahun gaba da suka kara da Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kwankwaso da Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa Hoto: @Saifullahihon
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan, wanda ya zo na huɗu a yawan kuri'u a sakamakon zaben da INEC ta ayyana, ya nemi zama kujera lamba ɗaya ne a inuwar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Kara karanta wannan

"Ba Daina Zuwa Wurin Shugaba Tinubu Ba Saboda Abu 1" Gwamnan PDP da Yaje Villa Sau 4 a Sati Ya Faɗi Dalili

Legit.nga Hausa ta tattaro cewa Kwankwaso ne ɗan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci shugaba Tinubu a Aso Rock tun bayan kammala babban zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan baku manta ba, a kwanakin baya rahotanni sun nuna cewa manyan 'yan siyasan biyu sun gana na tsawon awanni a birnin Faris na kasar Faransa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wannan ganawa ta yau Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023, ta kasance karo na biyu da Kwankwaso ya gana da Tinubu bayan na farko a watan da ya gabata ranar Litinin 25 ga watan Mayu.

Menene gaskuayar ganawar Kwankwaso da Tinubu a Faransa?

Wata majiya a cikin tawagar Kwankwaso ta tabbatar zaman taron a Faransa da cewa, "Eh tabbas sun gana da juna," inda ta ƙara da cewa amma a halin yanzu sun karkare tattaunawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wasu Kalamai

Haka zalika wata majiya a tsagin Tinubu, ta shaida wa Channels tv cewa:

"Eh dagaske ne, sun gana a Faransa kamar yadda aka rahoto, wannan wata babbar alama ce dake nuna Tinubu yana nan a raye kuma da lafiya."

Shugaba Tinubu Ya Gana da Sarakuna

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a Najeriya, Sultan ya yi jawabi mai jan hankali a wurin taron.

Ana tsammanin Tinubu zai taɓo batun haɗa kan kasa da kuma tsamo Najeriya daga yanayin da take ciki a zamansa da Sarakunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel