Kamar Almara: Zubin Gidan Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Girgiza Jama’ar Intanet

Kamar Almara: Zubin Gidan Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Girgiza Jama’ar Intanet

  • Watakila kun taba karanta tarihin rayuwar siyasar Sir Abubakar Tafawa Balewa, firayinministan farko kuma na karshe a Najeriya, amma; kun san a wane irin gida ya rayu?
  • A kafar Facebook, wani dan jaridar gantali, Pelu Awofeso ya ziyarci gidan marigayin da ke jihar Bauchi a Arewa maso Gabas
  • ‘Yan Najeriya da yawa sun shiga mamakin yadda gidan matsakaici yake da kyau, wanda a cewar dan Tafawa Balewa, an gina shi ne a shekarun 1950s

Jihar Bauchi Sir Abubakar Tafawa Balewa ne firayinministan farko da ba a yi na biyunsa ba a Najeriya, inda ya rike mukamin daga 1957 zuwa 1966.

Ya kasancewa na gaba-gaba wajen gwagwarmayar neman ‘yancin Najeriya, kuma fitaccen ne wajen iya sarrafa harshe, ga fasaha da iya turanci kamar baturen ingila.

Har yanzu, akwai abubuwa na tarihi da ke da alaka da marigayi Balewa, wadanda aka bari domin na baya su gani su shajja’u da halinsa.

Kara karanta wannan

An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni a Game da Talakawa

Yadda gidan Tafawa Balewa ya ba jama'a mamaki
Hoton gidan marigayi Tafawa Balewa | Hoto: Bauchi Friends Tours, @Sheikhhhweeder
Asali: Twitter

Daya daga cikin tsarin rayuwar Balewa mai ban mamaki akwai yadda ya rayu a gidansa da ke jihar Bauchi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gida ne matsakaici amma mai kyau da ke nuna tsantsar tawali’u da kankan da kai irin na dan siyasan zamanin baya.

Gidan Tafawa Balewa: Kwan wuta da makunnai tun na zamaninsa ne, inji Pelu Awofeso

A hotunan da ya yada a kafar Facebook Pelu ya bayyana yadda siffar gidan yake da kuma abubuwan da ya gani a ciki.

Hoton da ya yadan ya jawo hankalin jama’a, kasancewar gidan ya bambanta da irin na ‘yan siyasan zamani masu manyan gidaje a Abuja.

Ga dai abin da dan jaridan ya rubuta:

“Gidan Sir Tafawa Balewa, Bauchi. Na taka har cikin dakin zama, kuma na gagara cewa komai. Gaba daya kawazuci ya lullube ni. Kwan wutan, makunnai da sauran abubuwa dukkansu tun na farko ne.”

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Pelu ya bayyana cewa, ya hadu da dan marigayi Balewa, inda yace dan ya ce:

“A nan ne yake rayuwa tun kafin ya zama Firayinminista...An gina gidan nan ne a shekarun 1950s.”

Martanin jana'a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa game da gidan:

Ayodele Arigbabu:

"Ina kaunar tsarin ginin wancan zamanin, matsakaici amma mai kyau.”

Olanrewaju Tejuoso:

"Muhallin ya tuna min wani wuri mai kama da shi a Indonesia. Kamar almara.”

Olusegun Kayode Ajayi:

"Whaow! Wannan tsarin zanen gida akwai kyau.”

Chibuzor Sleekcheese Leopardi L'Infinito:

"Ya kamata a mai da wannan wurin gidan tarihi. Zai fi mana kyau mu kare tarihinmu ko kuma muna jiran turawan Yamma su zo su taimake mu bayan bautar damu? Wannan wuri yana da kyau.”

Makalarmu ta baya ta bayyana yadda aka yi juyin mulki a Najeriya har ta kai ga mutuwar Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel