Zaben Edo: Tsohon Ɗan Takarar Gwamma Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga PDP

Zaben Edo: Tsohon Ɗan Takarar Gwamma Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga PDP

  • Jam'iyyar PDP ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta da suka shafe shekaru suna mata aiki a jihar Edo
  • Tsohon ɗan takarar gwamna, Ken Imasuagbon, ya yi murabus, ya fice daga jam'iyyar PDP a wata wasiƙa da ya rubuta
  • Ya gode wa ɗaukacin shugabannin PDP, inda ya ce lokacin da ya shafe a cikin jam'iyyar ba zasu gushe a zuciyarsa ba

Edo - Tsohon ɗan takarar gwamna kuma babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Edo, Ken Imasuagbon, ya sanar da cewa ya fice daga jam'iyyar ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023.

Jaridar Punch ta tattaro cewa jigon siyasan ya tabbatar da matakin da ya ɗauka a wata takarda da ya aike wa shugaban PDP na jihar, Tony Aziegbemi.

Ken Imasuagbon.
Zaben Edo: Tsohon Ɗan Takarar Gwamma Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga PDP Hoto: punchng
Asali: UGC

Duk da haka, Mista Imasuagbon, bai bayyana ainihin dalilin da ya sa ya yanke fita daga jam'iyyar PDP ba cikin takardar murabus ɗin da ya rubuta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

Ya gode wa ɗaukacin shugabannin jam'iyyar PDP kuma ya kira zamansa a cikin jam'iyyar a matsayin wanda ba zai manta ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani sashin takardar ya ce:

"Tun shekarar 2007 da na shiga PDP zuwa yanzu wani lokaci ne da zan riƙa tunawa kuma ina ƙara gode wa Allah bisa ni'imarsa. Zama na a PDP ya bani damar haɗuwa da abokai da ba zan manta da zamana da su ba."
"Sai dai a rayuwar da muke ciki yanzu wani lokaci mutum zai yi tunanin yana son matsawa zuwa gaba. Bisa haka ina sanar da cewa na yi murabus daga kasancewa mamban PDP."
"Harwayau ina ƙara gode wa baki ɗaya shugabannin jam'iyyar PDP."

Taƙaitaccen tarihin zaman ɗan siyasan a PDP

Mista Imasuagbon, ya shiga tseren neman zama gwamna tun a shekarar 2007 bayan ya yi wa jam'iyyar PDP aiki tuƙuru ba dare ba rana.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

Amma a shekarar 2020, Mista Imasuagbon, da sauran 'yan takarar da suka nuna sha'awar zama gwamna sun janye wa gwamna Godwin Obaseki bayan ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Gwamnonin Jihohi a Abuja

A wani rahoton na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga taro da kafatanin gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Wannan ne karo na farko da sabon shugaban kasa ya gana da gwamnonin tun bayan kama aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel