"Ba Zai Yiwu ba," Hare Haren 'Yan Bindiga Sun Kai Mutane Makura a Jihar Sakkwato

"Ba Zai Yiwu ba," Hare Haren 'Yan Bindiga Sun Kai Mutane Makura a Jihar Sakkwato

  • Mutanen yankin karamar hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato sun harzuka kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga da suka raba su da gidajensu
  • Rahoton ya nuna cewa mutanen sun toshe babbar hanyar Sakkwato zuwa jihar Kebbi saboda tabarbarewar tsaro
  • Zanga-zangar ta jawo cunkoson ababen hawa na sa'o'i da dama a kan babban titin kafin jami'an tsaro su bude hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Hare-haren 'yan bindiga sun fusata mutanen da ke rayuwa a kauyukan karamar hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen da suka tsere daga ƙauyukansu sakamakon matsalar tsaro sun gudanar da zanga-zanga ranar Juma'a domin neman gwamnati ta kawo karshen hare-haren da ake kai musu.

Sokoto.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ce masu zanga-zangar, wadanda akasarinsu matasa ne, sun toshe babbar hanyar Sokoto–Yauri–Birnin Kebbi, suna neman gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna a Sokoto, sun kashe basarake, ɗansa da wasu mutane

Mutane sun mamaye babban titi a Sokoto

Matasan sun kunna wuta tare da shimfida itatuwa a kan hanyar, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa tare da barin daruruwan matafiya maƙale na tsawon sa'o'i.

Daga bisani jami'an tsaro sun yi nasarar tarwatsa zanga-zangar tare da bude hanyar da tsakar rana a yau Juma'a.

Lokacin da wakilai suka kai ziyara Bodinga, sun tarar da iyalai da dama da suka rasa matsugunansu suna samun mafaka a makarantu, masallatai da gidajen jama'a.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce zanga-zangar na da nufin jawo hankalin gwamnati kan tabarbarewar matsalar tsaro.

Ya ce:

"Ba za mu ci gaba da yin shiru ba yayin da ake kashe mutanenmu tare da tilasta musu barin gidajensu. Iyalai da dama da suka rasa gidajendu sun tsere zuwa garin Bodinga saboda ba su da wani wurin zuwa."

An jefi tawagar kakakin majalisar Sokoto

Wani shaidan gani da ido ya ce masu zanga-zangar sun yi ihu ga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, Tukur Bala Bodinga, tare da jifan tawagarsa da duwatsu lokacin da suka iso wurin.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Zamfara

Sai dai ya musanta rahotannin da ke cewa an lalata motar kakakin ko wata mota daga cikin tawagarsa.

"An yi ihu da jifan duwatsu, amma babu motar da aka fasa gilashinta ko aka lalata," in ji shi.

Karin mutane sun tsere daga kauyuka

Bayani sun nuna cewa mata da yara da tsofaffi da suka rasa mahallansu suna samun mafaka a wurare daban-daban a Bodinga.

Wasu na zaune a Makarantar Alhaji Sahabi Bodinga, Makarantar Dan Jeka, Makarantar Liman, Masallacin Mallam Bala, sabuwar kasuwar Bodinga da kuma garin Sifawa.

An ce mutanen sun fara kwarara zuwa Bodinga tun ranar Laraba bayan harin farko, yayin da sababbin hare-haren da aka kai daga ranar Alhamis zuwa safiyar Juma'a suka tilasta karin mutane tserewa.

A wani rahoton, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262