Gwamna Makinde Ya Fadi Abinda Tawagar G5 Ta Tattauna da Shugaba Tinubu

Gwamna Makinde Ya Fadi Abinda Tawagar G5 Ta Tattauna da Shugaba Tinubu

  • A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, 2023, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin G-5 na PDP a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
  • Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Samuel Ortom, Ifeanyi Ugwuanyi, Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu da Seyi Makinde
  • Awanni kaɗan bayan kammala wannan taron, abinda suka tattauna ya fara yawo a kafafen watsa labarai

FCT Abuja - Mambobin G-5 waɗanda aka fi sani da tawagar gaskiya na jam'iyyar PDP sun gana da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke Abuja.

Wannan ganawa da ta gudana ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, 2023, ta zo ne a daidai lokacin da ake kishin-ƙishin cewa sun fara shirin sauya sheƙa zuwa APC.

Tawagar G5.
Gwamna Makinde Ya Fadi Abinda Tawagar G5 Ta Tattauna da Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Me Tinubu ya tattauna da gwamnonin G-5?

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa tawagar G-5 ta ziyarci shugaba Tinubu ne domin yi masa bayani kan halin da ake ciki da manufarsu ta ganin an yi adalci da daidaito a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Bullo Kan Sa Labulen Tinubu da Gwamnonin da Suka Yaki Atiku a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde, wanda ke tare da sauran takwarorinsa da a yanzu sun sauka daga mulki, ya ce gina ƙasa ba karamin aiki bane, kuma yana buƙatar a riƙa binciken abinda ke wakana.

Ya ce tawagar G-5 zata ci gaba da zuwa wurin shugaban kasa a kokarin lalubo hanya mai ɓullewa a ƙasar nan, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Channels tv ta rahoto gwamna Makinde na cewa:

"Gina kasa babban aiki ne mai wahala, ya kamata ka riƙa kimantawa, ka san me kake aikatawa. Don haka zamu ci gaba da zuwa ganin shugaban kasa domin faɗa masa halin da ake ciki."
"Tawagar G-5 ta zo ne ta faɗa wa Tinubu manufar da ta tsayu a kai ta tabbatar da adalci da daidaito."

Buhari Ya Kashe Sama da Dala $19m da Dangote Ya Kashe Wajen Gyara Matatun Mai, Sule

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamnonin G5 Kan Wani Muhimmin Abu, Bayanai Sun Fito

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Sule ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta kashe sama da kuɗin da Ɗangote ya kashe da nufin gyara matatun Najeriya.

Ya ce har yau matatun ba su da amfani amma Ɗangote ya gina matatar da babu kamarta a Nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel