Ma'aikatar Bogi: Atiku Ya Tsoma Baki, Ya ba Tinubu Wa'adi don Gano Gaskiya
- Ana ci gaba da magana kan batun ma'aikatar PFIPC wadda gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta san da zamanta ba
- Dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sanya a gudanar da bincike
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa bayanan da fadar shugaban kasa ta yi, ba su warware shakkun da ake da shi kan lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ba Shugaba Bola Tinubu wa'adin kwanaki bakwai da ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya, kan badakalar hukumar PFIPC.
Atiku ya yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai ƙara rura wutar zargin jama'a na cewa wasu manyan mutane masu iko a gwamnati sun ci gajiyar lamarin.

Kara karanta wannan
Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya rika tarurruka da manyan jami'an gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne ta hannun babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Me Atiku ya ce kan lamarin?
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce takaddamar ta wuce batun zargin ƙirƙirar takardun bogi na yau da kullum, ta koma cikakkiyar matsala ta sahihancin hukumomi.
Atiku ya ce bayanin da fadar shugaban ƙasa ta bayar ta hannun Bayo Onanuga bai gamsar ba kuma ya bar tambayoyi da dama fiye da amsoshi.
Ya yi tambayar yadda mutum guda zai iya ƙirƙirar ofis don kansa, ya samu filin ofis a cikin ginin gwamnati, ya gudanar da tarurruka da tawagogin ofisoshin jakadancin ƙasashen waje, ya kai ziyarar ban girma zuwa hukumar EFCC, kuma ya riƙa sarrafa albashin ma'aikata ba tare da sanin kowa a gwamnati ba.
Atiku ya nuna shakku kan gwamnatin Tinubu
“Idan gwamnati tana son 'yan Najeriya su yi amanna cewa mutum guda ne da kansa ya ƙirƙiri ofis don kansa, ya samu filin ofis a cikin ginin gwamnati, ya gudanar da tarurruka da tawagogin ofisoshin jakadancin ƙasashen waje, ya kai ziyarar ban girma zuwa EFCC, ya sarrafa albashin ma'aikata, kuma ake zargin ya gudanar da asusu."
"Sannan ya gudanar da dukkan waɗannan ayyukan ba tare da sani, amincewa, sakaci, ko haɗin baki na kowa a cikin gwamnati ba, to wannan labarin yana ta da tambayoyi masu tayar da hankali da yawa fiye da yadda yake amsa su."
- Atiku Abubakar
Atiku ya nuna ayar tambaya
Ya ce kalaman Adeyemi, wanda ya musanta zargin kuma ya yi ikirarin cewa wasu manyan mutane suna ƙoƙarin rufe masa baki, ya sa gudanar da bincike mai zaman kansa ya zama tilas, The Punch ta kawo rahoton.
“Najeriya ta cancanci gaskiya. Yin bincike a asirce kan lamarin da kuma gyara kura-kurai zai fi kyau da gabatar da labari a bainar jama'a wanda bai gamsar ba saboda saɓanin da ke cikinsa."
"Dole ne shugaban kasa ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kuma mai zaman kansa cikin gaggawa. Duk wani abu da bai kai haka ba zai zama tamkar haɗin baki ne ta hanyar yin shiru."
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Adeyemi ya ce rayuwarsa na cikin hatsari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wanda ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin hatsari.
Adeniyi Adeyemi wanda ya yi magana daga ɓoye, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa tana ƙoƙarin rufe masa baki ne kawai.
Adeyemi ya yi ikirarin cewa rayuwarsa tana cikin haɗari, yana mai cewa hakan ya tilasta masa ɓoyewa domin ka da wani abu ya faru da shi.
Asali: Legit.ng

