Edo 2024: Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa LP

Edo 2024: Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa LP

  • Yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Edo a 2024, jam'iyyar PDP ta rasa babban jigonta, Kenneth Imansuangbon
  • Fitaccen ɗan siyasan ya sauya sheka zuwa Labour Party a hukumance kuma ya karɓi katin zama cikakken mamba
  • Ya ce jam'iyyar PDP ta mutu murus kuma da zaran ya karɓi tikitin takarar gwamna na LP, ta karewa APC

Abuja - Fitaccen ɗan siyasa a jihar Edo kuma tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Kenneth Imansuangbon, ya sauya sheka zuwa Labour Party (LP) a hukumance.

Jaridar Leadership da rahoto cewa Mista Imansuangbon ya shiga LP ne yayin da ake tunkarar babban zaben gwamnan jihar Edo, wanda ake hasashen fafatawa zata yi ɗumi a 2024.

Kenneth Imansuangbon.
Edo 2024: Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa LP Hoto: leadership
Asali: UGC

Imansuangbon, yayin da aka miƙa masa katin zama mamban LP, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta mutu murus.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Kara Jiƙa Wa PDP Aiki Kwanaki Kaɗan Bayan Rantsar da Tinubu

Shugaban Labour Party na kasa, Julius Abure, wanda kujerarsa ke tangal-tangal ne ya mika wa tsohon jigon PDP katin shaidar zama mamba a Abuja ranar Jumu'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi bayan karɓan katin, Mista Imansuangbon, ya ce:

"Babban abinda nake bukata shi ne sahihi kuma amintaccen zaben fidda gwani, matuƙar aka shirya sahihin zaɓe to ni zan lashe tikitin takarar LP. Ina karɓan tikiti, ta karewa PDP da APC."
"Dama PDP ta mutu murus, na tafi da ƙashin nasarar, daga nan zuwa 2024, LP zata kafa gwamnati a jihar Edo."

Daga karshe, Imansuangbon ya roki jam'iyyar Labour Party ta shirya zaben fidda gwani a bude babu wuru-wuru ta yadda kowa zai aminta da sakamakon, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ga fili da mai doki - Abure

Da yake nasa jawabin, shugaban LP na kasa, Julius Abure, ya ce zasu baiwa kowa damar baje kolinsa a zaben fidda gwanin da zasu shirya nan gaba a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

"Zamu buɗe ƙofa kowa ya taka wasa, muna da misalai da dama da zamu nuna, lokacin da muka shirya zaben fidda gwani a Anambra, ba'a taɓa ganin irinsa ba."

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa

A wani labarin na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa na sahun gaba da suka kara da Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel