Lokaci Ya Yi Da Za a Samu Shugabar Kasa Mace a Najeriya, Obasanjo

Lokaci Ya Yi Da Za a Samu Shugabar Kasa Mace a Najeriya, Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya goyi bayan mika ragamar shugabancin kasar ga mata
  • Obasanjo wanda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samu shugabar kasa mace ya ce ta haka ne za a samu ci gaba a Najeriya
  • A cewarsa, ya kamata a gwada shugaba mace don ganin kamun ludayin jinsin wajen jan ragamar harkoki a kasar

Ogun - A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga samun shugabar kasa mace a Najeriya.

Obasanjo ya yi magana ne a wani taro da ya gudana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
Lokaci Ya Yi Da Za a Samu Shugabar Kasa Mace a Najeriya, Obasanjo Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Da yake jawabi, Obasanjo ya ce yana goyon bayan kudirin, cewa ya kamata a baiwa mace dama don a ga kamun ludayinta.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

An an yi adalci tsakanin jinsi sannan Najeriya za ta ci gaba, Obasanjo

A cewarsa, sai an mika mulki tare da raba shi daidai a tsakanin jinsi ne sannan kasar za ta samu ci gaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obasanjo ya ce:

"A nawa ra'ayin, idan muna so kasar ya bunkasa, ya kamata mu duba jinsi bibbiyu, saboda hannu daya baya iya daukar jinka.
"Kana iya yin yadda ka so, amma ya kamata ayi shi yadda ya kamata, muna iya samun karin gogewa daga jinsi bibbiyun, menene banbanci tsakanin jinsin? Kawai dai mata na iya samun ciki na tsawon watanni tara ne sannan su maza ba sa iya wa. Wannan ne kawai banbancin da ke tsakaninmu.
"A ganina, babu wani abu da zai hana mace zama shugabar kasarmu."

Ya kamata a sako mata a harkar siyasa, mataimakiyar gwamnan Ogun

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Daga Karshe Tsohon Minsitan Buhari Ya Nemi Gafarar Tsohon Gwamna Da Wasu, Ya Ce Sharrin Shaidan Ne

Da take goyon bayan Obasanjo, mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, Naimot Salako-Oyedele, ita ma ta yi kira ga kawo mata cikin harkar siyasa, rahoton The Nation.

A cewarta, yan tsirarun mata ne ke mulki a kasar nan, tana mai cewa haka abun yake a jihar Ogun.

Yan sanda sun farmaki gidan tsohon gwamnan Zamafara, Matawalle, sun kwato motoci

A wani labari na daban, mun ji cewa an kwato wasu manyan motoci daga gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

An tattaro cewa an kama manyan motocin ne yayin wata mamaya da aka kai gidan Matawalle da ke GRA a Gusau, a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel