Yadda BVAS Ta Gaza Tura Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Jami'in INEC

Yadda BVAS Ta Gaza Tura Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Jami'in INEC

  • Biyu daga cikin shaidun da PDP ta gabatar game da zaben shugaban kasa sun amince cewa na'urar BVAS ta gaza tura sakamakon bayan kammala kidaya
  • A cewar shaidun, BVAS ta riƙa nuna 'Error' da zaran ta kammala tura sakamakon zaɓen 'yan majalisun tarayya
  • Ma'aikatan INEC na wucin gadi sun bayyana cewa bisa tilas suka bi wata hanyar haɗa sakamakon bayan sun gano BVAS ba zata iya komai ba

Ma'aikatan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) na wucin gadi sun yi bayani a matsayin wani ɓangaren shaidun jam'iyyar PDP a kotun sauraron ƙorafin zaben shugaban ƙasa.

A jawabinsu, ma'aikatan wucin gadi su biyu, sun amince da cewa na'urar BVAS ta gaza tura sakamako ga INEC kai tsaye ranar zaben shugaban kasa bayan kammala kidaya kuri'u.

Yakubu.
Yadda BVAS Ya Gaza Tura Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Jami'in INEC Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Shaidun sun faɗa wa Kotu cewa na'urar da aka ba su ta nuna 'Error' watau alamar akwai damuwa jim kaɗan bayan sun tura sakamakon zaben Sanata da ɗan majalisar tarayya cikin sauki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Jaridar Punch ta rahoto cewa shaidun, Friday Egwuma da Grace Timothy, sun yi wannan bayani ne ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, 2023 a Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban kasa mai zama a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

BVAS ta gaza tura sakamako - Ma'aikatan INEC

Jami'an INEC ɗin na wucin gadi sun ƙara da cewa dole suka bi wata hanyar na haɗa sakamakon zaɓen bayan fahimtar cewa BVAS ba zata taimaka masu da komai ba, Tribune ta tattaro.

A halin yanzun, shugaban kwamitin alkalan dake sauraron ƙarar, mai shari'a Haruna Tsammani, ya ɗaga zaman zuwa gobe Jummu'a, 9 ga watan Yuni, 2023.

Idan baku manta ba, a zaman sauraron karar zaben 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya fara gabatar da shaidu a gaban Kotun domin tabbatar da cewa an tafka kura-kurai.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP da Ɗumbin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa

Gwamnan Enugu Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Ya Sako Nnamdi Kanu

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana wasu daga cikin batutuwan da suka tattauna yayin ganawa da shugaba Tinubu.

Ya ce daga ciki, ya roki shugaban ya duba yuwuwar sako shugaban ƙungiyar yan aware da aka ayyana da ta yan ta'adda IPOB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel