Shugaban Ƙasa, Tinubu, Ya Sa Labule da Gwamnonin G5 a Aso Rock

Shugaban Ƙasa, Tinubu, Ya Sa Labule da Gwamnonin G5 a Aso Rock

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gana da mambobin tawagar G-5 waɗanda suka yaƙi Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023
  • Gwamna Seyi Makinde na Oyo da tsoffin gwamnoni huɗu da suka kafa G5 duk sun halarci taron a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis
  • Gwamnan Enugu na yanzu, Peter Mbah, ya halarci taron wanda har yanzu ba'a bayyana abinda suka tattauna ba

Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar PDP 5, waɗanda suka ɓalle daga inuwar babbar jam'iyyar adawa suka kafa tawagar G-5.

Channels tv tattaro cewa gwamnoni 4 daga cikin 5 sun sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, yayin da ɗaya daga cikinsu ya samu nasarar ta zarce zuwa zango na biyu.

Tawagar G5.
Shugaban Ƙasa, Tinubu, Ya Sa Labule da Gwamnonin G5 a Aso Rock Hoto: channelstv
Asali: UGC

Rahoto ya nuna dukkan mambobin tawagar G-5, wanda suka haɗa da gwamna mai ci da tsoffin gwamnoni 4 sun halarci ganawar a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Yanzu- Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Wasu Gwamnonin PDP, Bayanai Sun Fito

Waɗanda suka halarci ganawa da shugaban ƙasan sun haɗa da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsoffin gwamnoni, Nyesom Wike (Ribas), Samuel Ortom (Benuwai), Okezie Ikpeazu (Abiya) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika gwamnan jihar Enugu na yanzu, Peter Mbah, na cikin waɗanda aka gani sun shiga ganawa da Bola Tinubu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Yadda G5 ta yaƙi Atiku da shugaban PDP na ƙasa

Gabannin huɗu daga ciki su miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, gwamnonin PDP guda 5 sun haɗa kai sun kafa tawagar da suka raɗa wa suna G-5 a takaice bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.

Tawagar ta buƙaci shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus, sannan a maye gurbinsa da ɗan kudu, haka ne kaɗai sharaɗin da zai sa su marawa Atiku Abubakar baya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Gwamnonin Jihohi 36 a Karon Farko, Bayanai Sun Fito

Amma Atiku, wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP da Ayu sun kira gwamnonin da mayaudara kuma suka sa ƙafa suka shure buƙatar kafin ranar zaɓe.

A lokuta da dama a ciki da wajen Najeriya, shugaba Tinubu ya gana da Wike na jihar Ribas da kuma gwamna Makinde na Oyo kafin zuwan ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Bamu Yarda Akwai Wani Tallafin Man Fetur Ba a Najeriya, ASUU

A wani labarin na daban kuma ASUU ta bayyana matsayarta kan batun tallafin man fetur wanda ake ta cece-kuce.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce tuntuni ba su yarda akwai wani abu mai sun tallafin mai ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel