Siyasar Najeriya
APC na shirin mamaye kananan hukumomin FCT a zaɓen ciyamomi na 2026 da 2027, tare da tsananta dabarun jawo 'yan adawa. INEC za ta gudanar da zaɓen FCT a Fabrairu.
Tawagar Dr. Bala Maijama'a Wunti ta ziyarci ofisoshin yan sanda bayan matashi mai suna Adamu Salisu ya hau kan karfen sadarwa a Bauchi saboda ɗan siyasa.
EFCC ta gano manyan 'yan siyasa na amfani da 'yan 'yahoo-yahoo' wajen safarar biliyoyin kuɗin sata zuwa waje. EFCC ta ce hakan ya haifar da kunya ga Najeriya.
Ministan sadarwa a mulkin Buhari, Adebayo Shittu ya yi gargadi kan batun ajiye Kashim Shettima a 2027. Ya ce APC za ta shiga rudani idan aka ajiye Shettima.
Mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya bayyana cewa bisa tsari, Shugaba Tinubu ke da ikon zaɓen wanda zai zama abokin takararsa a 2027.
Mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum.ya karyata labarin da kw yawo cewa ya gama shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Tsohon hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Aliyu Audu, ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru don ganin an kawo karshen mulkinsa a zaben shekarar 2027.
Hadimin shugaban APC, Oliver Okpala ya yi magana kan harin da wasu 'yan jam'iyyar suka kai wa Abdullahi Umar Ganduje a jihar Gombe kan Sanata Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya fito ya yi magana kan shirin da ake zargin yana yi na ficewa daga PDP zuwa APC. Ya ce jita-jita ce kawai marar tushe.
Siyasar Najeriya
Samu kari