Shettima a 2027: Ministan Buhari Ya Yi Gargadi bayan APC Ta Shiga Rudani

Shettima a 2027: Ministan Buhari Ya Yi Gargadi bayan APC Ta Shiga Rudani

  • Maganar sauya mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima a zaɓen 2027 na cigaba da tayar da kura a jam’iyyar APC
  • Taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas a Gombe ya rikide ya koma tashin hankali bayan an kaurace wa ambato sunan Shettima
  • Jagororin jam’iyyar sun fito fili sun ce Bola Tinubu da Shettima za su ci gaba da kasancewa tare, yayin da ake gargadi kan haɗarin rushewar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar rikici da rabuwar kai yayin da jita-jita ke yawo cewa ana shirin sauya mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a zaɓen 2027.

A taron shugabannin jam’iyyar a Arewa maso Gabas da aka yi a Gombe, rashin ambaton sunan Shettima a jawabai biyu na manyan jam’iyyar ya tayar da tarzoma da zargin ƙulla makirci.

Maganar takarar Shettima a jawo rudani
APC ta shiga rudani kan takarar Shettima a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Kashim Shettima|Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Punch ta rahoto cewa tsohon ministan sadarwa a lokacin shugaba Muhammadu Buhari, Adebayo Shittu ya yi magana kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar sauya Shettima ta tada kura a Gombe

Mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa daga Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya ambaci Bola Tinubu a matsayin ɗan takara, amma bai kira Shettima ba a matsayin abokin tafiyarsa ba.

Hakan ya tayar da hankali, inda wasu suka mamaye wurin taron tare da duka da jifa har aka ga Salihu na tserewa.

Bayan sa, shugaban jam’iyyar ƙasa Dr. Abdullahi Ganduje ya gabatar da jawabi amma shi ma bai bayyana goyon bayansa ga Shettima ba, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.

Wasu daga cikin mahalarta taron har sun yi barazanar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa PDP idan har aka cire Shettima daga tikitin takara.

Dalori ya ce Shettima na nan daram

Mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa, Ali Bukar Dalori ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a cire Shettima daga tikitin takarar Tinubu.

Ya ce:

“Ba mu ga wani laifi da ya aikata da zai sa a sauya shi ba.”

Shi ma Ganduje ta bakin hadiminsa, Cif Oliver Okpala, ya bayyana harin da aka kai masa a taron a matsayin rashin kishin kasa da rashin tunani.

Vanguard ta wallafa cewa ya kara da cewa,

“Wannan ba kawai hari bane a kan Ganduje, harin ne a kan jagorancin jam’iyya gaba ɗaya.”

Maganar ministan Buhari kan ajiye Shettima

Tsohon minista a gwamnatin Buhari, Adebayo Shittu ya gargadi APC da kada ta kuskura ta cire Shettima, yana mai cewa hakan zai iya tarwatsa jam’iyyar gaba ɗaya.

“Idan ba a samu matsala ba, me ya sa za a fara maganar gyara?”

A martaninsa, Mustapha Salihu ya bayyana cewa ba shi ba ne ke da hurumin zaɓar mataimaki, face shugaban ƙasa ne ke da ikon hakan idan ya samu tikitin jam’iyya.

Ministan Buhari ya gargadi APC kan ajiye Shettima
Ministan Buhari ya gargadi APC kan ajiye Shettima. Hoto: Adebayo Shittu
Asali: Facebook

Maganar fadar shugaban kasa kan Shettima

A wani rahoton, kun ji cewa rade radin da ake na sauya mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a 2027 ta tayar da kura.

Daya daga cikin hadiman shugaba Bola Tinubu da ya fito daga jihar Borno, Daniel Bwala ya ce ba su da masaniya kan ajiye Shettima.

Batun ajiye Shettima ya fara daukar hankali sosai ne yayin da aka yi taron APC a Arewa maso Gabas, yankin da mataimakin shugaban kasa ya fito.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng