Matsala Ta Tunkaro Tinubu, Tsohon Hadiminsa Ya Fadi Shirin da Yake Yi Masa a 2027

Matsala Ta Tunkaro Tinubu, Tsohon Hadiminsa Ya Fadi Shirin da Yake Yi Masa a 2027

  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan dalilin da ya sanya ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Aliyu Audu ya bayyana cewa ya fice daga gwamnatin Tinubu ne domin ya samu damar yaƙarsa a zaɓen da za a yi a 2027
  • Tsohon hadimin shugaban ƙasan ya nuna cewa zai yi aiki tuƙuru don ganin cewa an raba shi da kujerar shugabancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Shawara na musamman kan harkokin jama’a, Aliyu Audu, ya bayyana dalilin yin murabus ɗinsa.

Aliyu Audu ya bayyana cewa ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu ne domin ya samu damar aiki tuƙuru wajen ganin ba a sake zaɓen shugaban ƙasan ba a 2027.

Aliyu Audu ya yi magana kan ficewa daga gwamnatin Tinubu
Aliyu Audu ya ce zai yi don kifar da Tinubu a 2027 Hoto: Aliyu Audu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Aliyu Audu ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirrin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa hadimin Tinubu ya yi murabus?

Ya ce dalilansa na ficewa daga gwamnati sun samo asali ne daga abin da ya kira “tsayin daka kan akida” da kuma burin ganin an gina Najeriya wadda za a riƙa damawa da kowa.

“Na ɗauki wannan mataki ne bisa gaskiya da aƙida, da kuma rayuwa wadda ke da ma’ana fiye da son kai. Na yarda cewa Najeriya ba ta yi lalacewar da ba za a iya gyarata ba."
“Ina da ƙarfin gwiwar yanke shawara ko da kuwa zai janyo min cikas a gaba. Ko da makoma ba ta da tabbas, zan fi so na fuskanci rashin tabbas a gobe fiye da zama cikin mugunta a yau."

- Aliyu Audu

Aliyu Audu ya soki gwamnatin Tinubu da zargin fifita ramuwar gayya fiye da haɗin kan ƙasa, yana mai cewa gwamnatin ta kauce daga alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya kuma yi nuni da dangantakar siyasa da ke tsakanin Shugaba Tinubu da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, wacce ya ce a da tana da amfani amma yanzu ta zama mai cike da shakku.

Shugaba Tinubu ya samu abokin adawa a 2027
Aliyu Audu zai yi aiki don kifar da Tinubu a 2027 Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Wane shirin tsohon hadimin Tinubu yake yi?

Da aka tambaye shi ko furucin da Tinubu ya yi ne kan maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya ne ya janyo ya fice daga gwamnati, sai ya kada baki ya ce:

"Furucinsa ya tabbatar da abin da nake zargi a zuciyata. Ya kuma ƙarfafa ni wajen yanke shawarar cewa ba zan sake mara masa baya a 2027 ba."
"Ba zan iya ci gaba da zama cikin gwamnatinsa yayin da a zuciyata nake shirin kifar da shi ba. Saboda zan yi."
“Da yardarAllah, za mu cire Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. Za mu mayar da shugabanci hannun mutanen da jama’a suka zaɓa, ba wanda aka tilasta ba."

- Aliyu Audu

Tinubu ya magantu kan tsarin jam'iyya ɗaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya taɓo batun maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ko kaɗan bai da wani shiri na ganin cewa Najeriya ta koma ƙarƙashin tsarin jam'iyya ɗaya.

Bola Tinubu ya nuna cewa ba ya ganin tsarin jam'iyya ɗaya abu ne mai kyau ga dimokuraɗiyyar Najeriya, amma ba zai kulle ƙofa ga masu son shigowa cikin APC ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng