Gwamnan Plateau Ya Shirya Ficewa daga PDP zuwa APC? Ya Tsage Gaskiya
- Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
- Caleb Mutfwang ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar mai cewa ya shirya komawa jam'iyyar APC
- Gwamnan ya nuna cewa ba zai ci amanar mutanen jihar Plateau ba ta hanyar ficewa daga jam'iyyar da ya lashe zaɓe a ƙarƙashinta a 2023
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana kan jita-jitar cewa yana shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa ba shi da wata niyyar sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Jos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kan shirin sauya sheƙarsa, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙarya marar tushe, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Wannan bayani na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun sauya sheƙar wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC, ciki har da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno.
Haka kuma, wasu ƙungiyoyi daga cikin jam’iyyar APC sun yi kira ga Gwamna Mutfwang da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki, abin da ya haifar da rikici da cacar baki tsakanin manyan jam’iyyun guda biyu a jihar Plateau.
Mutfwang ya musanta shirin barin PDP
A yayin tattaunawar, Gwamna Mutfwang ya ƙaryata jita-jitar, yana mai cewa jihar Plateau jiha ce da PDP ta daɗe da zama tushenta, kuma barin jam’iyyar zai zama cin amana ga jama’ar jihar.
“Ina faɗa muku gaskiya, ban taɓa yin wata tattaunawa da kowa ba game da barin PDP don komawa APC. Kafafen yada labarai sun yi hasashe da yawa, amma babu abin da ya faru."
"Akwai kungiyoyi biyu ko uku da ke yaɗa wannan jita-jita. Ɗaya daga cikinsu na da kyakkyawar niyya. Sun san APC ba ta taɓa samun karɓuwa a jihar Plateau ba. Da gaske na ke faɗin hakan, sun hau mulki ne kawai ta hanyar zamba."
“A shekarar 2015, ba su lashe zaɓen ba. Rikicin da ya mamaye PDP ne ya janyo wasu suka yi wa jam'iyyar zagon ƙasa, amma ko a wancan lokacin, APC ba ta ci zaɓe ba."
"A lokacin ina shugaban ƙaramar hukuma ne. Mun dakatar da ƙirgar ƙuri’u da ƙarfe 8:00 na dare don ci gaba washegari. Amma da na farka da misalin ƙarfe 2:00 na dare don yin fitsari, sai na ji an riga an bayyana sakamakon."
- Gwamna Caleb Mutfwang

Asali: Facebook
Meyasa gwamnan ba zai koma APC ba?
Gwamna Mutfwang ya ce zai zama rashin imani ya ci amanar jama’ar da suka tsaya tsayin daka tare da PDP.
“Shi ya sa kullum nake cewa Allah ne da mutanen Plateau za su yanke hukunci kan makomar siyasa ta. Duk inda mutanen Plateau suka nufa, can za mu tafi."
“A gare mu, wannan ba ma wani batu ba ne da ya kamata mu tattauna. Ni cikakken mamba ne na PDP. Kuma ina nan daram. Ina da yaƙinin cewa nan ba da daɗewa ba, rikicin PDP zai zama tarihi."
- Gwamna Caleb Mutfwang
Fani-Kayode ya soki gwamnan Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya soki gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang.
Femi Fani-Kayode ya yi wa gwamnan raga-raga ne bisa karɓar baƙuncin jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman da ya yi a gidan gwamnatin jihar Plateau.
Tsohon ministan ya bayyana tarbar jakadan Isra'ila da gwamnan ya yi, ya saɓawa ɗabi'u da koyarwar addinin Kirista.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng