2027: Gagarumin Shirin da APC Ta Yi na Murkushe PDP, LP a Birnin Tarayya Abuja

2027: Gagarumin Shirin da APC Ta Yi na Murkushe PDP, LP a Birnin Tarayya Abuja

  • Jam’iyyar APC ta tsananta dabarun karɓar ikon dukkanin kananan hukumomi shida a Abuja a zaɓen ciyamomi na 2026 da ke tafe
  • APC na shirin kwace kujerar sanata da kuma ta majalisar wakilai daga LP, inda ta jaddada ƙudurin rushe mulkin PDP da LP a Abuja
  • Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da shugaban AMAC, na jan hankalin 'yan adawa zuwa ga jam’iyyarsu gabanin zaɓen 2026/2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Jam’iyyar APC ta tsananta dabarun ta na karɓar ikon dukkanin kananan hukumomi shida da ke a babban birnin tarayya Abuja a zagaye na gaba na zaɓen ciyamomi.

A wata sanarwa da ta fitar kwanan nan, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen Abuja a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Jam'iyyar APC ta ce ta shirya kwace dukkanin kananan hukumomin Abuja a zaben ciyamomin da ke tafe
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abuja tana da kananan hukumomi shida, waɗanda suka haɗa da kwaryar Abuja (AMAC), Bwari, Abaji, Gwagwalada, Kuje da Kwali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta shirya cin zaben ciyamomin Abuja

Manyan shugabannin APC sun tabbatar da cewa jam’iyyar za ta lashe dukkan kananan hukumomin shida, wanda yin hakan zai ƙara mata damar riƙe mulki a babban zaɓen 2027.

Baya ga shirye-shiryen karɓar kujerun ciyamomi da na kansiloli a Abuja, APC tana shirin karɓar kujerar sanata ɗaya tilo a yankin, wacce a halin yanzu take hannun Sanata Ireti Kingibe ta jam’iyyar LP.

Har ila yau, ta nuna sha’awar karɓar ɗaya daga cikin kujerun majalisar wakilai guda biyu, watau mazaɓar tarayya ta Bwari/AMAC, wacce ita ma tana ƙarƙashin ikon jam’iyyar LP.

Idan ba a manta ba, jam’iyyar APC ta dade da rike ikon mazaɓar tarayya ta Kuje/Kwali/Abaji/Gwagwalada.

Za mu rusa mulkin PDP da LP – APC

Da yake bayar da dalilan da suka sa jam’iyyar ta kuduri aniyar karɓar Abuja, daraktan yaɗa labaran jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ya ce PDP ta daɗe tana mulkin FCT.

Ya kuma ce kudurin shine jam’iyyar APC ta karɓe birnin tare da isar da dimokuraɗiyya ga al’umma daidai da kudurin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu.

Bala Ibrahim ya ce:

“Kada ku manta, ministan Abuja, wanda ma ba ɗan APC bane, ya ce zai yi aiki don nasarar babbar jam’iyyarmu. Don haka burinmu shine mu mamaye ko ina, ciki har da Abuja.
“A shirye muke. Mun yi duk abin da ya kamata a yi don mu shiga zsaɓen. An tantance ‘yan takara, kuma jam’iyyar za ta goyi bayan su.”
APC ta ce Wike ya yi alkawarin taimakawa nasarar jam'iyyar a zabuka masu zuwa
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Dabarun lashe zaben jam'iyyar APC

An ce jam’iyyar APC tana kara tasiri wajen jawo manyan 'yan jam’iyyun adawa zuwa gare ta gabanin zaɓen ciyamomin Abuja na 2026 da babban zaɓen 2027.

Kwanan nan, shugaban AMAC, Christopher Zakka Maikalangu, ya jagoranci dubban 'yan PDP, kansiloli 12 da kuma ɗumbin abokan siyasa zuwa APC gabanin zaɓen.

A wajen taron, Abdullahi Ganduje da Sanata Barau Jibrin sun ce APC za ta karɓe dukkan kananan hukumomi kuma za ta cika alkawuran Renewed Hope Agend na Tinubu.

Tinubu, Wike za su yi babban aiki a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin kaddamar da fara aikin gina sabuwar hediwatar hukumar zaɓe ta kasa (INEC) a Abuja.

Hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA), ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike, ce ta shirya wannan aikin domin bikin cikar Shugaba Tinubu shekara biyu a kan mulki.

Sai dai wannan lamari ya fara tayar da jijiyoyin wuya, inda ra'ayoyin lauyoyi suka bambanta game da wannan aikin gina ofishin INEC gabanin zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.