Bayan Amincewa da Kudurorin Haraji, Majalisa Ta Tura wa Shugaban Kasa don Rattaba Hannu

Bayan Amincewa da Kudurorin Haraji, Majalisa Ta Tura wa Shugaban Kasa don Rattaba Hannu

  • Majalisar dokokin kasar nan ta sanar da cewa tuni ta kammala aikin gyara kudurorin haraji da shugaban kasa, Bola Tinubu ya aika mata a bara
  • Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ya ce an yi aiki na tsanaki da lura a kan dukkanin kudurorin
  • Ya kara da cewa yanzu haka, an tura wa Shugaba Tinubu kudurorin haraji da ta amince da su domin ya rattaba hannu su zama doka a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Dokokin Najeriya ta ce ta kammala aiki kan kudurorin dokar haraji da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike mata a bara.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Majalisa ta kammala aiki a kan kudurorin haraji Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Sanata Adaramodu ya tabbatar da hakan a ganawa da 'yan jarida, inda ya kara da cewa yanzu haka an tura su zuwa fadar shugaban kasa domin a sanya wa hannu su zama doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta kammala nazari kan kudirin haraji

Sanata Adaramodu ya ce majalisa ta yi cikakken nazari da gyare-gyare kan kudurorin kafin amincewa da su a hukumance tare da aikewa da su zuwa ofishin shugaban kasa.

Jaridar Punch ta wallafa Sanatan ya ce:

“Eh, yanzu kudurin ya bar hannunmu, yana kan hanyarsa ta zuwa wajen Shugaban Kasa domin ya sanya masa hannu ya zama doka.
“Kudurorin haraji irin wadannan suna bukatar taza da tsifa sosai. Dole ne bangarorin masana shari’a a majalisun biyu su tabbatar da cewa kudurorin sun yi daidai da dokokin kasa kafin su tura wa Shugaban Kasa."

Yadda aka duba kudirorin haraji a majalisa

Sanata Adaramodu ya kara da cewa duba kudurorin ba aikin gaggawa ba ne, saboda hakan yana bukatar kulawa da gyare-gyare daidai da tsarin doka.

Majalisa ta amince da kudurorin haraji
Majalisa ta aika kudurorin haraji ga shugaban kasa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

“Ba aiki ba ne na kwana biyu ko uku. Bayan an kammala aikin daidaita su kuma Akwun Majalisar Dokoki ta Kasa zai mayar da su kundi daya. Bayan haka ne kawai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su sa hannu a aike da su,”

Kafin amincewa da kudurorin, sun janyo muhawara mai zafi a zaurukan Majalisar Wakilai da ta Dattawa, har ma da fadin kasar baki daya, inda masana da 'yan siyasa suka yi ta tofa albarkacin bakinsu.

Majalisa ta amince da kudirorin haraji

A baya, mun kawo labarin cewa Majalisar Dattawa ta amince da biyu daga cikin kudurorin dokar gyaran haraji guda huɗu da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar gabanta a bara.

Wadannan kudurori sun samu amincewar sanatoci ne bayan dogon nazari da suka yi a kan rahoton kwamitin wucin gadi da Sanata Sani Musa na jihar Neja ke jagoranta.

Dokokin da aka amince da su sun hada da dokar kafa Hukumar Haraji ta Najeriya da kuma Dokar kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji, yayin da shugaban kasa ya ce dokokin za su inganta Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.