Damagum: Shugaban PDP na Ƙasa na Shirin Sauya Sheka zuwa APC? Bayanai Sun Fito
- Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC
- A wata sanarwa da hadiminsa ya fitar, ya ce maƙiyan Damagum ne ke yaɗa labarin mara tushe saboda sun gaza cimma burinsu
- Sanarwar ta ce wasu ƴan siyasa da suka gaza samun nasara a zaɓukan shugabannin PDP ne ke yaɗa wannan rahoton na karya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya karyata jita-jitar cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.
Damagum ya danganta irin waɗannan rahotanni da makiyansa na siyasa, waɗanda ya ce suna cikin ɓacin rai da ƙoƙarin ɓata masa suna.

Asali: Twitter
“Makiyana ne ke yaɗa wannan labari,” in ji Damagum cikin amsar da ya bai wa jaridar The Nation ta hanyar sakon tes kan raɗe-raɗin da ke yawo a soshiyal midiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Damagum na shirin fita daga PDP zuwa APC?
Damagum ya tabbatar da cewa babu wani shiri da yake yi a ɓoye na sauya sheka daga PDP zuwa APC kafin zaɓen 2027.
Ana zargin Damagum na shirin ficewa daga PDP da zaran wa’adin rikon da aka ba shi ya ƙare a gangamin jam’iyyar na ƙasa da aka tsara gudanarwa daga 28 zuwa 30 ga Agusta, 2025.
Amma a wata sanarwa da mai taimaka masa, Nuru Jos, ya fitar, Damagum ya danganta jita-jitar da wasu ’yan siyasa da suka gaza kai labari a zaɓukan shugabannin PDP da aka yi a Yobe.
Damagum ya faɗi waɗanda yake zargi a PDP
Ya zargi waɗanda ke yaɗa rahoton da yunkurin bata masa suna, kawo cikas ga shugabancinsa a PDP, da kuma rikita kokarinsa na sasanci da gyara jam'iyya.
A rahoton Leadership, sanarwar ta ce:
“Ofishin muƙaddassin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya samu labarin wani rahoton karya da wata majiyar da ba a san ta ba ta yaɗa, wanda ke zargin cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa APC.
"Wannan rahoto maras tushe, wanda wasu da ba a san su ba suka rubuta, an ƙirƙire shi ne don bata sunan shugaban PDP, Ambasada Damagum."

Alakar jita-jitar Damagum da tarukan PDP
Sanarawar ta ƙara da tabbatar da cewa tarukan zaɓen shugabanni da PDP ta gudanar a mazaɓu, kananan hukumomn da shiyyar Arewa maso Gabas da aka yi a Yobe sun gudana cikin nasara.
"Abin takaici wasu da suka gaza kai labari a waɗannan zaɓuka, sun koma ƙirƙiro ƙarya da nufun ɓata muƙaddashin shugaban jam'iyya mai aiki tuƙuru.
"Wannan yunƙurin bata suna ya fito ne daga ɓangaren masu yi wa PDP zagon ƙasa, waɗanda suka gaza cimma burinsu, tare da zargin Damagum da tare masu a hanya," in ji sanarwar
Gwamnan Filato na shirin komawa APC?
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa yana shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar mai cewa ya shirya komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Ya bayyana cewa Filato jiha ce da PDP ta daɗe da gina tushenta, yana mai cewa barin jam’iyyar zai zama tamkar cin amana ga jama’ar da suka zaɓe shi a 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng