Bayan Ya Sha da Kyar, Shugaba a APC Ya Ƙara Kinkimo Faɗa kan Batun Cire Shettima a 2027
- Kwamred Mustapha Salihu ya bayyana cewa shugaban ƙasa ke da ikon yanke wanda zai zama abokin takararsa a zaɓen 2027
- Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Gabas ya ce sun yanke shawarar mara wa Bola Tinubu baya ba tare da sharaɗi ba
- Ya ce kundin tsarin mulki tikiti ɗaya ya sani na shugaban ƙasa, amma batun mataimaki kuma sai wanda ɗan takara ya zaɓa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya sake neman tayar da rikici kan batun tikitin APC a 2027.
Mustapha ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kaɗai ke da ikon yanke hukunci ko Kashim Shettima zai sake kasancewa abokin takararsa a 2027 ko a’a.

Asali: Twitter
Jagoran APC ya faɗi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na Channels TV a ranar Litinin,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi ƙarin haske kan rigimar da ta faru a taron masu ruwa da tsakin APC a Arewa maso Gabas lokacin da aka amince Tinubu ya yi takara ba tare da ambatar Shettima ba.
Arewa maso Gabas na tare da Bola Tinubu
A cewar Mustapha Salihu, jiga-jigan APC na shiyyar sun yanke shawarar mara wa Tinubu baya ba tare da wani sharaɗi ba, duk da cewa Shettima ɗan yankin ne kuma mai rike da mukamin mataimakin shugaban ƙasa.
“Ba za mu ce saboda ɗan mu ne Mataimakin Shugaban Ƙasa sai mu ɗora wa Asiwaju wani sharaɗi ba. Mun mara masa baya ne ba tare da wata ƙa’ida ba.
"A tsarin mulki tikiti ɗaya gare mu, babu wani tikitin mataimakin shugaban ƙasa. Idan muka ce dole sai mun jinginawa Asiwaju, muka ware muka goyi bayan Shettima, to fa kamar muna riga malam masallaci ne.
- Mustapha Salihu.
Mustapha ya caccaki jiga-jigan APC
Mataimakin shugaban APC ya soki wasu daga cikin jiga-jigan siyasa da ke kawo hayaniya da tashe-tashen hankali a taruka don ƙoƙarin nuna tasirinsu na siyasa, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce irin wannan salon siyasa tuni ya zama tarihi, inda ya ƙara da cewa:
“Wasu har yanzu suna siyasar irinta 1979. An wuce nan a siyasa, yanzu muna cikin zamanin da barazana da hatsaniya ba su karawa mutum farin jini," In.ji shi.

Asali: Twitter
Duk da haka, ya jaddada cewa suna alfahari da Kashim Shettima a matsayin ɗan Arewa maso Gabas, suna mutunta shi, kuma suna goyon bayansa amma ikon cire shi ko tafiya da shi na hannun Shugaba Tinubu.
Arewa ta amfana da manufofin Shugaba Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa ɗan kwamitin yakin neman zaben APC a 2023, Ahmed Dankabo ya ce yankin Arewa ya fi kowa amfana da manufofin Tinubu.
Dankabo ya bayyana nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen 2023 a matsayin wani babban sauyi da zai iya ama.alheri ga Najeriya.
Ya ce cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗin waje matakai ne masu amfani da za su inganta rayuwar talakawan Najeriya
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng