APC Ta Tsage Gaskiya kan Batun Goyon bayan Ribadu Ya Maye Gurbin Shettima
- APC reshen jihar Adamawa ta fito ta nesanta kanta daga batun marawa Nuhu Ribadu baya don neman wani muƙamin siyasa
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin da aka yaɗa masu nuna hakan
- Kalaman APC na zuwa bayan an fara hasashen wasu jiga-jiganta daga Adamawa na son a maye gurbin Kashin Shettima da Ribadu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta yi martani kan batun cewa ta goyi bayan Nuhu Ribadu don neman wani muƙamin siyasa.
APC ta ƙaryata rahotannin da ke cewa tana goyon bayan Mallam Nuhu Ribadu don nenan wani muƙamin siyasa a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Hong kwanan nan.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na jihar Adamawa, Muhammed Abdullahi, ya sanya wa hannu, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar APC ta bayyana rahoton a matsayin “ƙirkirarren labari” da ya juya ma’anar haƙiƙanin manufar taron da kuma abubuwan da suka biyo baya.
Ya ce taron wani ɓangare ne na zagayen da jam’iyyar ke yi don tallata kanta a matakin ƙananan hukumomi a faɗin jihar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
An yi hasashen maye gurbin Shettima da Ribadu
A baya-bayan nan, akwai rikici a sashen Arewa Maso Gabas na jam’iyyar APC dangane da makomar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027.
A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Lahadi, shugabannin jam’iyyar daga jihar Borno sun nemi a tabbatar da Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan yunƙurin wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar Adamawa na son ganin Ribadu ya maye gurbin Shettima.
Jam'iyyar APC ta musanta goyon bayan Ribadu
Sai dai reshen jam’iyyar APC na jihar Adamawa ya musanta irin wannan yunƙuri.
"Hankalinmu ya kai kan wani rahoto da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai dangane da zargin mara wa Mallam Nuhu Ribadu baya don neman wani muƙamin siyasa."
“Muna so mu bayyana a fili cewa rahoton ba gaskiya ba ne, kuma ya sauya haƙiƙanin manufar abubuwan da suka wakana a taron da aka yi a Hong."
“An gudanar da taron ne a ci gaba da zagayen da muke yi a ƙananan hukumomi don karfafa mambobinmu da kuma isar da matsayar jam’iyya cewa Shugaba Tinubu ya cancanci ƙarin wa’adi na shekaru huɗu."
- Muhammed Abdullahi
APC ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da Ribadu
APC ta ce duk da cewa an kaɗa ƙuri’ar amincewa da aikin Mallam Nuhu Ribadu, a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, hakan bai nufin an mara masa baya don wani muƙamin siyasa ba.

Asali: Facebook
“Muna alfahari da irin yadda Mallam Ribadu ke gudanar da aikinsa. A matsayin wanda shugaban ƙasa ya nada, yana aiki da mutunci da nagarta.”
“Shi ya sa muka kaɗa ƙuri’ar amincewa da aikinsa, ba wai domin muƙamin siyasa ba."
- Muhammed Abdullahi
Jam’iyyar ta buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da duk wani ƙoƙari na karkatar da gaskiya ko kawo rashin haɗin kai a APC.
Ƴan APC sun yi wa Abdullahi Ganduje ihu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a yankin Arewa maso Gabas, ya bar baya da ƙura.
A wajen taron wasu mambobin APC sun yi wa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ihu.
Hakan ya biyo bayan bambance-bambancen ra'ayoyi da aka samu a wajen tron wanda aka gudanar a jihar Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng