Siyasar Kano
Kungiyar tsofaffin 'yan majalisar dokokin jihar Kano ta nada Sanata Barau Jibrin matsayin uban kungiya. Barau Jibrin ya ce zai cigaba da aiki domin kawo cigaba.
Yayin da ake jita-jitar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC, jam'iyyar a Kano ta bukaci tsohon gwamnan ya nemi gafarar Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Jam'iyyar NNPP ta musa ikirarin da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje na cewa Rabiu Kwankwaso zai koma APC bayan mutuwar NNPP. NNPP ta ce zancen ba gaskiya ba ne.
Hoton da ake yaɗawa na Rabiu Kwankwaso sanye da hula mai ɗauke da tamabarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba gaskiya ba ne, kirkirarsa aka yi.
Shugaban APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce kofar jam'iyyar a bude take ga kowa, musamman ga masu kishin kasa da ci gaba inda ya yi gargadi da gindaya sharuda.
Shugaban tsagin NNPP a Kano, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce sun san da ganawar Abdullahi Ganduje da 'yan majalisar jam'iyyar da suka hada da Kawu Sumaila.
Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa ya fara neman shawarwari kan kiran da ake masa na komawa APC.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai dawo APC saboda NNPP ta mutu murus a Najeriya. Ganduje ya ce masu shirin hadaka za su wargaje.
Babbar kotun jihar Kano ta bayyana cewa za ta sanar da ranar yanke hukunci jan bukatar ɓamgaren waɗanda ake ƙara a shari'ar da gwamnatin Kano ke tuhumar Ganduje.
Siyasar Kano
Samu kari