Abubuwa na Neman Rikicewa Saudiyya, Hare Haren Mayakan Houthi Sun Yi Gagarumar Barna
- Rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ta ce hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Houthi sun yo barna
- Hare-haren sun shafi biranen Khamis Mushait, Abha da Taif, inda aka lalata gidaje bakwai da motoci biyu
- Wani tsohon jami’in diflomasiyyar Amurka ya ce Washington na iya ci gaba da tallafa wa Saudiyya da bayanan sirri da horo, ba tare da shiga yaƙin kai tsaye ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Riyadh - Rundunar haɗin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ta ce hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da dakarun Houthi suka kai Saudiyya sun jikkata fararen hula 13.
Hare-haren sun faru ne a ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026, inda aka kai hari kan wasu wuraren fararen hula a biranen Khamis Mushait, Abha da Taif.

Source: Getty Images
An lalata gidaje da motoci
Kakakin rundunar haɗin gwiwar, Manjo Janar Turki al-Maliki, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafin X.
Ya ce hare-haren sun haddasa raunuka daga ƙanana zuwa matsakaita ga fararen hular da abin ya shafa.
Hakazalika, Manjo Janar Turki al-Maliki ya ce harin ya kuma lalata gidaje bakwai da motoci biyu.
Al-Maliki ya ce ci gaba da kai hare-haren da ya kira na ganganci na nuna salon ƙungiyar Houthi da akidarta ta tsattsauran ra’ayi wajen ƙara rura wutar rikici da kai hari kan fararen hula da wuraren da suke amfani da su.
Ya ce rundunar haɗin gwiwar za ta ɗauki matakin da ya dace kuma mai ƙarfi domin kare ikon Saudiyya, kadarorin fararen hula da kuma rayukansu.
Kakakin ya ce za a yi hakan ne bisa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ƙa’idar kare kai da ke cikin Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Amurka ba za ta shiga yaƙin kai tsaye ba

Kara karanta wannan
Akwai kura: Hare haren jirage marasa matuka sun jawo gagarumar matsala a Saudiyya
William Lawrence, farfesa a Jami’ar American kuma tsohon babban jami’in diflomasiyyar Amurka, ya ce da wuya Amurka ta shiga yaƙin Yemen kai tsaye cikin ɗan gajeren lokaci.
Da yake magana da tashar Al Jazeera, Lawrence ya ce ci gaba da gwabza yaƙin ba lallai ne ya kawo zaman lafiya cikin sauri ba. Ya ce a maimakon haka, yaƙin na iya ƙara jinkirta samun mafita.
Amurka na tallafa wa Saudiyya
Lawrence ya ce rawar da Amurka ke takawa a rikicin ita ce samar wa Saudiyya da bayanan sirri, sa ido, taimakon yanke shawara da horar da jami'an soji kan amfani da makamai. Ya kwatanta wannan tallafin da irin taimakon da Iran ke bai wa Houthi.
Sai dai ya ce da wuya Amurka ta shiga aikin soji kai tsaye, saboda hakan na iya ƙara tsananta rikicin tare da tsawaita yaƙin maimakon rage shi.

Source: Getty Images
Saudiyya ta kai hare-hare a Yemen
A wani labarin kuma, kun ji cewa jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kusan 40 kan wasu yankuna 4 da ke kasar Yamen.
Rahotanni sun nuna cewa an kai hare-haren ne a gundumomin As-Salif da At-Tuhayta, da kuma tsibirin Kamaran da ke Yemen.
Asali: Legit.ng
