Sarkin Musulmi Ya Bayar da Shawara kan Mutanen da Za a Zaba a 2027
- Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya shawarci ’yan Najeriya su yi nazari kan alkawuran ’yan siyasa kafin yanke shawarar wanda za su zaɓa a 2027
- Ya gargadi ’yan siyasa da kada su mayar da matsalar tsaro da sauran ƙalubalen ƙasa kayan yaƙin neman zaɓe
- Sarkin ya bukaci jam’iyyu su gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, tare da mai da hankali kan batutuwan da za su kawo haɗin kai da ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shawarci ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan wajen tantance alkawuran ’yan siyasa kafin su yanke shawarar wanda za su zaɓa a babban zaɓen 2027.
Sarkin Musulmi ya kuma gargadi ’yan siyasa da kada su mayar da matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta wani makami na siyasa yayin yakin neman zaɓe.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya kawo sabon tsarin tallafi da zai taimaki 'yan Najeriya

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce sarkin ya yi wannan magana ne ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026 lokacin da ya karɓi tawagar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen 2027 na jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul-Aziz Yari Abubakar, a fadarsa da ke Sokoto.
Sarkin Musulmi ya shawarci masu zaɓe
Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ya kamata masu zaɓe su saurari alkawuran ’yan siyasa da kyau a lokacin yakin neman zaɓe.
Ya bukaci ’yan Najeriya su yanke shawarar wanda za su zaɓa bisa abin da suke ganin zai fi amfani gare su da kuma ƙasar baki ɗaya.
Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga jam’iyyu da ’yan takararsu su gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, tare da mai da hankali kan batutuwa masu muhimmanci.
Ya ce ya kamata ’yan siyasa su mutunta zaɓin masu kaɗa ƙuri’a, tare da gudanar da siyasa ta hanyar da za ta ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci gaba.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
Sanata Yari ya nemi shawarar Sarkin Musulmi
Tun da farko, Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Sanata Abdul-Aziz Yari, ya ce tawagar ta kai ziyara fadar Sarkin Musulmi ne domin neman shawararsa, jagorancinsa na uba da addu’o’insa gabanin zaɓen 2027.
Sanata Yari ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna kishin ci gaban Arewa da Najeriya tun kafin ya zama shugaban ƙasa, ta hanyar tallafa wa shugabanni da ayyukan ci gaba.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC na da nasarori da dama da za ta gabatar wa ’yan Najeriya, musamman waɗanda aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Yari ya tabbatar wa Sarkin Musulmi cewa APC za ta gudanar da yakin neman zaɓe cikin lumana, tare da roƙon ci gaba da goyon bayansa da addu’o’insa.

Source: Original
Sarkin Musulmi ya musanta cewa a zabi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar yaɗa labarai ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta yi martani kan batun goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.
Tawagar ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Asali: Legit.ng