Asiri Ya Fara Tonuwa: An Kama Mutum 2 kan Kashe Danshagamu a Kano
- Yan sandan jihar Kano sun sami nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum a yankin Gaida
- Rahoto ya ce maharan sun kutsa cikin gidan mamacin ne a daren Litinin inda suka farmake shi da kayan aiki masu kaifi
- Kwamishinan yan sandan jihar ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamacin tare da tabbatar da gudanar da bincike mai zurfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu da ke da zama a unguidar Gaida a karamar hukumar Kumbotso.
Kamar yadda rundunar ta bayyana, a ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2026 da misalin karfe 11:30 na dare ne ta samu rahoton gaggawa daga 'yan banga yankin Gaida game da farmakin da aka kai wa mamacin.

Source: Facebook
Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a Facebook ta bayyana cewa tsagerun ne suka kutsa gidan mamacin da karfi sune kuma suka masa da rauni da abubuwa masu kaifi.
Matakin da aka ɗauka
Bayan samun wannan labari, jami'an rundunar daga shiyyar Kumbotso suka hanzarta zuwa wajen da abin ya faru inda aka gaggauta daukar mamacin zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammad da ke Kano inda aka ce ya rasu.
Bayan samun umarni daga Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar shugabannin al'umma sun gudanar da gagarumin bincike wanda ya kai ga kama mutane biyu da ake zargi.
A yanzu haka ana ci gaba da amsa tambayoyi daga bakin wadanda aka kaman gami da tattara shaidu domin gano ainihin manufar kai wannan hari.
Jawabin kwamishinan 'yan sanda
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ya nuna alhini game da aukuwar lamarin sannan ya mika sako na ta'aziyya ga iyalan mamacin.
Ya sake jaddada aniyar rundunar ta gano dukkan masu hannu a ayyukan laifuffuka domin fuskantar shari'a.
"Rundunar 'yan sandan jihar Kano ba za ta yi kasa a aiki ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Muna tabbatar wa al'ummar Kano cewa za a bi wa mamacin hakkinsa,"
In ji CP din.

Source: Original
An kama dan sandan bogi
A wani labarin daban, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani mutum mai shekaru 35, Adamu Musa, bisa zarginsa da yin sojan gona a matsayin babban jami'in 'yan sanda yana cutar al'umma.
Wanda ake zargin, wanda mazaunin unguwar Kureken Sani ne a Kano, an kama shi ne ta hannun jami'an 'yan sanda na bangaren Panshekara a ranar 1 ga Satumba, 2026 sakamakon bayanan sirri da rundunar ta samu.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai inda ya ce an samu nasarar kama shi ne bayan rahoton gaggawa.
Asali: Legit.ng

