Rigimar ADC Ta Hayayyafa a Gidan Atiku, Jam’iyya Ta Samu Shugabanni 3 Lokaci Guda

Rigimar ADC Ta Hayayyafa a Gidan Atiku, Jam’iyya Ta Samu Shugabanni 3 Lokaci Guda

  • ADC ta rabu kashi uku a Adamawa biyo bayan rantsar da Dr. Markus Peter Danbaki a matsayin sabon shugaban jam'iyya
  • Sabon shugaban ya amsa rantsuwar ofis tare da yi wa mambobin jam'iyya alkawarin tafiya da kowa a reshen Adamawa
  • Dama can Hassan Muhammad wanda shi ne mataimakin sakataren ADC na kasa, ya ajiye mukaminsa gaba daya a jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Adamawa - Rikicin cikin gidan ADC ya karu ne a maimakon ya lafa, yanzu haka an rantsar da wani sabon shugaba a Adamawa.

A karshen makon da ya gabata ne aka rantsar da Dr. Markus Peter Danbaki a matsayin shugaban ADC na reshen jihar Adamawa.

Atiku Abubakar
'Dan takaran ADC a zaben shugaban kasa lokacin karbar tuta Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Shugabannin jam'iyyar ADC sun zama 3 a Adamawa

Wannan lamari ya jawo bangarorin jam’iyyar sun kai uku a jihar Adamawa, mahaifar ‘dan takarar shugaban kasa a cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Kafin bayyanar tsagin Dr. Markus Peter Danbaki, ana fama da rikici ne tsakanin Sadiq Dasin mutanen Alhaji Sa’idu Naira a ADC.

Kowane bangare ya dage cewa shi ne halataccen shugaban jam’iyyar ADC a Adamawa.

An rantsar da sabon shugaban ADC a Adamawa

Mai ba wani tsagin taware na ADC shawara ta fannin shari’a, Barista Ibrahim Ahmad, ya ba Dr. Markus Danbaki rantsuwar kama aiki.

An yi wannan taro ne gaban wasu ‘ya ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma iyalansu a garin Yola a karshen mako.

Da yake jawabi gabanin shiga ofis, Markus Danbaki ya yi alkawarin zai tafi da kowa, ba zai jagoranci jam’iyyar adawar shi kadai a jihar ba.

Markus Danbaki ya ce rashin adalci ya jawo jam’iyyar ta samu kan ta a cikin matsala.

Nafiu Bala ya sake dasa wa ADC matsala

Sabon shugaban ya kuma yi alkawari zai dage wajen hada-kan ‘ya ‘yan ADC, ya shawo kan duk masu neman takara a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Hotunan yadda aka gudanar da jana'izar Bamanga Tukur a Adamawa

Yana sa ran a karkashinsa, jam’iyyar ADC ta yi nasara a babban zabe mai zuwa na 2027.

Haka zalika ya sanar da mubaya’arsa ga shugabancin Alhaji Muhammad Shuwa da Nafi’u Bala a matakin jiha da kuma na kasa.

Daily Post ta rahoto yadda abubuwa suka cabe wa jam’iyyar hamayyar a Adamawa makonni bayan an rasa wasu manyan 'yan siyasa.

An ce ya samu wannan kujera ne bayan wata wasika da sakataren jam’iyya, Zubairu Ishaq Mohammed, ya aika masa a Agusta.

Zubairu Ishaq Mohammed ya sanar da Danbaki cewa an nada shi ya jagoranci ADC a jihar.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar mai neman zama shugaban kasa tare da wasu mutanensa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Mataimakin sakatare na kasa ya bar ADC

A lokacin da ake wannan ne shi kuma Mataimakin sakataren ADC na kasa, Hassan Muhammadu ya rubuta takardar murabus dga jam'iyyar.

Hassan Muhammadu ya ajiye mukaminsa kuma ya rabu da jam’iyyar ADC a jihar Gombe, yana mai godiya ga damammakin da ya samu.

ADC: Rikicin takara gwamna ta barke a Adamawa

An ji labari rikici ya barke a jam'iyyar ADC ta jihar Adamawa sakamakon zargin sauya sunan ɗan takarar gwamna Umar Suleiman (Omarana).

Kara karanta wannan

An gindaya wa Nyesom Wike sharuɗa 2 game da APC kafin zaben 2027

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya zargi bangaren Atiku Abubakar da hannu wajen canza 'dan takaran jam'iyyar.

Shugabannin kwamitin yakin neman zaben Omarana sun ƙaryata batun cewa takarar su ta koma hannun Modibbo Hamman Tukur Ribadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng