Kwankwaso Ya Kwatowa NNPP Mawakin Kwakwasiyya da Ya Koma APC Ta Hannun Barau

Kwankwaso Ya Kwatowa NNPP Mawakin Kwakwasiyya da Ya Koma APC Ta Hannun Barau

  • Fitaccen mawakin tafiyar siyasar Kwankwasiyya, Abubakar Sani ya sake sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar NNPP
  • Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya karɓi Abubakar Sani a gidansa da ke titin Miller a Kano
  • A kwanakin bayan, an ji mawakin ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC yayin da ya ziyarci Sanata Barau Jibrin a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mawakin Kwankwasiyya, Abubakar Sani Dan Hausa, wanda a baya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, ya sake komawa tafiyar Kwankwasiyya.

Dawowar tasa na zuwa ne bayan watanni da ya shafe a APC karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Kwankwaso
Abubakar Sani ya koma NNPP bayan sauya sheka zuwa APC. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda Abubakar Sani ya koma NNPP ne a wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa ya tarbi Abubakar Sani a gidansa da ke titin Miller a Kano, inda ya bayyana jin dadinsa kan dawowar ɗan gwagwarmayar daga APC.

Baya ga haka, Kwankwaso ya kai ziyara ofishin NNPP na jihar Kano da ke Lugard Road, Nasarawa GRA, domin ƙarfafa matsayin jam’iyyar a jihar.

NNPP: Kwankwaso ya karbi Abubakar Sani

Abubakar Sani ya kasance daya daga cikin mawakan Kwankwasiyya masu kishin tafiyar NNPP kafin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC.

Ya sauya sheka zuwa APC ne lokacin da ya ziyarci Sanata Barau Jibrin a Abuja watanni da suka wuce.

Sai dai da alama abubuwa ba su tafi daidai da tsammaninsa ba a APC, lamarin da ya sanya ya sake komawa gida.

A cikin wata sanarwa daga bangaren Kwankwasiyya, an bayyana dawowar Abubakar Sani a matsayin komawa gida.

Tun a lokacin da Abubakar Sani ya koma APC wasu 'yan Kwankwasiyya suka rika cewa mawakin zai dawo tafiyar NNPP a gaba kadan.

Kwankwaso ya ziyarci ofishin NNPP Kano

A wani bangaren, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara mai muhimmanci zuwa ofishin NNPP na jihar Kano a yau Talata.

Ziyarar ta gudana ne domin ƙarfafa tushen NNPP da kara shirin jam’iyyar wajen tunkarar manyan zabuka masu zuwa.

Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyyar na jiha da kuma wasu daga cikin mambobi masu kishin tafiyar Kwankwasiyya.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade radin cewa madugun Kwankwasiyyar zai koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Kwankwasi
Kwankwasiyya ya ziyarci ofishin NNPP a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Shugabannin APC daga matakin kasa da jihar Kano sun yi tsokaci kan lamarin, amma duk da haka Sanata Rabiu Kwankwaso bai ce komai ba har yanzu.

Alakar APC da NNPP a jihar Kano

A cikin 'yan watannin nan, alaka tsakanin jam’iyyun NNPP da APC a jihar Kano ta shiga wani mawuyacin hali, musamman bayan sauyin sheka na fitaccen mawakin Kwankwasiyya, Abubakar Sani Dan Hausa.

Wannan sauyin, wanda daga baya ya zama dawowa gida, ya nuna irin rashin jituwa da rashin daidaito da ke tsakanin manyan jam’iyyun biyu a jihar.

Abubakar Sani ya kasance ɗaya daga cikin masu kishin tafiyar NNPP kafin sauya shekarsa zuwa APC, amma dawowarsa ya jaddada cewa abubuwa ba su tafi daidai ba a sabuwar mafakarsa.

Sau da yawa ana fassara sauyin sheka da dawo da irin waɗannan mambobi a matsayin alamar rashin daidaito ko rashin cika alkawari daga ɗaya bangaren.

Hakan na ƙara bayyana cewa akwai babban gibi tsakanin tsarin tafiyar siyasa da jin daɗin mambobi a cikin APC, wanda hakan ke haifar da komawa NNPP.

Haka zalika, ziyarar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ofishin NNPP a Kano da karɓar Abubakar Sani a gidansa, na nuni da ƙoƙarin NNPP na ƙarfafa matsayinta a jihar da kuma rage tasirin APC, musamman a gabanin manyan zaɓuka.

Wannan alaka mai cike da takaddama na ci gaba da jan hankali a siyasar Kano.

Barau ya karbi 'yan NNNP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya karbi wasu 'yan Kwakwasiyyya zuwa jam'iyyar APC a Abuja.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa mutanen sun koma APC ne saboda ayyukan alheri da yake gabatarwa a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

Jibrin ya kara da cewa a yanzu haka NNPP na raguwa a Kano sosai kuma wasu daga cikin manyan 'yan jam'iyyar na shirin komawa APC a gaba kadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng