Kano: An Tsallake Kwankwaso, Shekarau an ba Barau Uban Kungiyar Tsofaffin 'Yan Majalisa

Kano: An Tsallake Kwankwaso, Shekarau an ba Barau Uban Kungiyar Tsofaffin 'Yan Majalisa

  • Tsofaffin 'yan majalisar dokokin Kano sun nada mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, a matsayin uban kungiyarsu
  • Sun bayyana cewa sun yanke hukuncin ne saboda irin hazaka, kishin kasa da kuma gudummawar da ya bayar ga cigaban Kano
  • Sanata Barau Jibrin ya yi godiya tare da shan alwashin ci gaba da sadaukar da kansa don ganin an kawo cigaba da jin dadin al’umma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Kungiyar tsofaffin 'yan majalisar dokoki ta jihar Kano ta karrama mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da ta ba shi matsayin uban kungiya.

Shugaban kungiyar, Kwamared Alhassan Uba Idris, tare da sakatarenta, Umar S. Muhammad, sun ce an yi haka ne saboda nagartaccen jagoranci da Barau Jibrin ke nunawa a majalisa.

Barau
Kungiyar tsofaffin 'yan majalisar Kano ta ba Barau matsayi. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin 'yan majalisar sun ce gudummawar Sanata Barau wajen ci gaban Kano da Najeriya ta zarce kima, kuma hakan ya sa suka ba shi wannan matsayi domin kara karfafa masa guiwa.

Barau ya yi godiya da alkawarin kara kokari

Sanata Barau Jibrin ya bayyana farin cikinsa tare da nuna godiya bisa wannan gagarumar karramawa da aka masa.

Barau Jibrin ya ce:

“Ina matukar godiya da kuka ga na cancanci wannan matsayi. Insha Allah, ba zan ba ku kunya ba.”

Ya kara da cewa a matsayinsa na dan majalisa kuma dan kasa mai kishin al’umma, zai ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da cigaba, musamman a fannin walwala da jin dadin al’umma.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce:

“Cigaban Kano da Najeriya gaba daya yana kan gaba a ajandarmu.”

Barau
Barau ya ce zai cigaba da kawo cigaba a Najeriya. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Twitter

’Yan Najeriya sun taya Barau murna

Bayan bayyanar matsayin da aka ba Sanata Barau, mutane da dama sun nuna farin cikinsu a shafukan sada zumunta.

Muhammad Abdullahi Abu Sulaim ya rubuta cewa:

“Ina taya ka murna... kwarewarka ta shugabanci ta musamman ce. Ko da ba dan asalin Kano ba ne ni, ina kaunarka saboda yadda kake wakiltar Arewa gaba daya.”

Yusuf Abdullahi Shehu kuwa ya ce:

“Masha Allah, ka cancanta da hakan, shugabanmu.”

Ashiru Abubakar Turaki ya kara da cewa:

“Manufar ita ce mu hada kai, mu yi aiki tare. Ina taya ka murna.”

Kungiyar tsofaffin 'yan majalisar ta bayyana cewa Barau ya kafa tarihin zama daya daga cikin 'yan majalisa mafi tasiri, inda ya kawo kudurori da dama da suka inganta rayuwar jama’a.

Kungiyar ta bukaci Sanata Barau da kada ya yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da wakiltar muradun jama’ar Kano da Najeriya baki daya.

Hausawan Legas sun goyi bayan Barau

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya samu goyon bayan kungiyar Hausawa da ke zaune a jihar Legas.

'Yan kungiyar sun bayyana cewa Sanata Barau na ciki 'yan majalisa da suke nuna kwarewa da kawo cigaba a Najeriya.

A yayin ziyarar da suka kai masa a birnin tarayya Abuja, sun tabbatar wa Barau cewa za su cigaba da goyon bayan ayyukan da yake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng