InnalilLahi: An Shiga Har Gida An Kashe Fitaccen Mai Magana kan Siyasa a Jihar Kano

InnalilLahi: An Shiga Har Gida An Kashe Fitaccen Mai Magana kan Siyasa a Jihar Kano

  • An kashe fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa na jihar Kano, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa
  • Yan uwansa sun ce wasu mutane da har yanzu ba a gano su ba sun kai wa marigayin hari bayan sun kutsa gidansa, inda suka yanka shi har lahira
  • Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Nigeria ta yi kira ga rundunar yan sanda da ta gudanar da bincike tare da hukunta makasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa an kashe fitaccen mai sharhin siyasa da ke Kano, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa da ke jihar Kano, lamarin da ya jefa mabiyansa da al'ummar jihar cikin jimami.

'Yan uwa sun ce wasu mutane da har yanzu ba a gano su ba sun kai wa marigayin hari bayan sun kutsa gidansa, inda suka yanka shi har lahira.

Kara karanta wannan

Kiran da Ahmad Gumi ya yi wa gwamnati bayan dambarwar matar Morocco

Dan Shagamu.
Fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil Dan Shagamu Hoto: Ibrahim Khalil Dan Shagamu
Source: Facebook

An yi wa Danshagamu kisan gilla

Babbar yayarsa, Aisha Muhammad Lawal, ta shaida wa Daily Trust cewa danta ya samu kira da misalin karfe 12:30 na dare, inda aka sanar da shi abin da ya faru.

Ta ce:

“Wasu mutane da har yanzu ba a gano su ba sun kutsa gidansa suka yanka shi har lahira. Ban kasance a wurin ba, don haka ban san abin da ya faru ba, sai na nemi dana ya je wurin.
"Da ya isa, ya tarar da 'yan sanda a wurin. Sun garzaya da shi asibiti, sun gudanar da wasu bincike, daga bisani suka mika gawarsa gare mu da misalin karfe 2:30 na dare.”
“Ban san ainihin abin da ya faru da yadda lamarin ya faru ba. Amma an sanar da ni cewa an kama mutane biyu daga yankin. Yana da mata da 'ya'ya shida. Muna kira ga gwamnati ta taimaka mana wajen tabbatar da an yi adalci.”

Kara karanta wannan

Mata na cikin alheri, an fara raba tallafin N50,000 ga wadanda suka cancanta a jihar Kano

Iyalan marigayin sun ce ba sa zargin wani mutum ko wasu mutane na musamman, amma sun dage cewa dole ne a yi adalci.

Amnesty ta tabbatar da lamarin

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Nigeria ce ta tabbatar da mutuwarsa a shafinta na X ranar Laraba inda ta ce an tsinci gawarsa cikin wani tafkin jini a cikin gidansa.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai bayyana shi a matsayin mummunan aika-aika.

Ta bukaci hukumomin Najeriya da su gaggauta gudanar da bincike kan abubuwan da suka kai ga mutuwarsa tare da tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka aikata kisan a gaban kuliya.

Amnesty ta ce an yi masa kisan gilla

Amnesty International ta ce:

"An yi masa kisan gilla bayan wadanda suka kashe shi sun yi galaba a kansa."

Amnesty International ta kuma nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin karuwar barazana da tsoratarwa da ke da alaka da siyasa yayin da zabe ke kara karatowa.

Kungiyar ta ce:

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Matar Morocco ta fito ta fadi abin da ya faru da kanta a bidiyo

"Yayin da zabe ke kara karatowa, muna ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali game da barazanar kisa da ke da alaka da siyasa da kuma tsoratarwa."

A wani labarin, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262