Wata Sabuwa: Amurka Ta Binciki Wasu Masu Alaka da Tinubu, Ta Kwace Makudan Kudi
- Reno Omokri ya amince cewa FBI ta gudanar da bincike kan wasu mutane masu alaƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Jakadan Najeriya da aka naɗa zuwa Mexico ya ce Shugaba Tinubu ba shi ne wanda aka yi bincike a kansa ba a lokacin
- Ya kuma yi kira da kada a fitar da bayanan sirri daga takardun binciken da hukumomin Amurka ke riƙe da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jakadan Najeriya da aka naɗa zuwa Mexico, Reno Omokri ya tabbatar cewa Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta taɓa gudanar da bincike kan wasu mutane masu alaƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Omokri ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba shi ne asalin wanda hukumomin Anurka suka gudanar da bincike a kansa ba.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television ranar Lahadi da ta gabata.
Omokri ya fadi binciken da FBI ta yi
Ya ce cece-ku-ce da ke tattare da wasu bayanan Amurka ya samo asali ne daga abin da ya kira rashin fahimta kan alaƙar Tinubu da wasu kuɗaɗen da hukumomin Amurka suka yi wa bincike.
A cewarsa, a lokacin Tinubu yana aiki a matsayin akanta kuma yana riƙe da kuɗaɗen wasu abokan hulda waɗanda a kansu ne Amurka ta yi bincike.
“An gudanar da bincike. Bola Ahmed Tinubu ba shi ne wanda ake bincike a kansa ba,” in ji Omokri.
Ya bayyana cewa daga baya an ƙwace kuɗaɗen da ake magana a kansu bayan an gano cewa akwai alamun suna da matsala, yana mai jaddada cewa matakin ya shafi asusun ne, ba Tinubu da kansa ba.

Kara karanta wannan
An fara fito da abubuwan da Tinubu ya shirya yi a Najeriya idan ya lashe zaben 2027
“Shugaban ƙasa akanta ne, sannan yana da kuɗaɗen abokan ciniki. FBI ta tuhumi waɗannan mutanen, kuma sakamakon haka ta ce tana zargi wasu kuɗaɗe.
“Daga nan, lokacin da aka sanar da shugaban, shugaban ya amince a ƙwace kuɗaɗen. Abin ya shafi asusun ne, ba shugaban kasa ba.”

Source: Twitter
Me hukumar FBI ta gano?
Omokri ya kuma ambaci wata takardar FBI ta 2003, wadda ya ce ta ƙunshi sakamakon binciken da aka gudanar kan Tinubu, yana mai cewa bayanan sun nuna cewa babu wani tarihin kama shi da laifi ko sammacin kama shi.
Sai dai ya amince cewa ba za a iya musanta cewa FBI ta gudanar da bincike ba, yana mai nanata cewa Tinubu ba shi ne mutumin da ake bincike a kansa ba.
Jakadan da aka naɗa ya ƙi bayyana sunayen mutanen da aka bincika, yana mai cewa ba ya son fallasa iyalansu ga sakamakon da ba dole ba, cewar rahoton Vanguard.
Dalilin Tinubu na hana fitar rahoton FBI
Kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa Bola Ahmed Tinubu ba ya son hukumomin Amurka su sako rahotonsa.
Fadar shugaban kasar ta ce Tinubu ya dauki wannan matakin ne dogaro da hakkokin kariya da dokar FOIA ta Amurka ta tanada.
Fadar ta ce shari'ar da ke gaban Kotun Tarayya ta Amurka mai zaman kanta a rikici ne na farar hula da ke bukatar neman samun bayanan gwamnati amma ba ya da alaka da laifi.
Asali: Legit.ng

