'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Harin da Ya Jawo Asarar Rayuka da Kona Gidaje
- 'Yan ta'adda da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari Bitirhuya da ke ƙaramar hukumar Hong a Adamawa, inda suka kashe mutane
- Maharan sun shiga garin da babura tsakanin ƙarfe 5:00 zuwa 6:00 na yammacin Lahadi, inda suka rika harbi tare da tilasta wa mutane guduwa
- Shugaban ƙaramar hukumar Hong ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe tare da yin kira ga jama'a su taimaka wa jami’an tsaro wajen gano masu aikata laifuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Hatsabiban da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Bitirhuya da ke ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa, inda suka kashe mazauna yankin huɗu tare da ƙona gidaje da dama.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne kasa da mako guda bayan da ’yan ta’addan sun kashe mutane 12 a ƙauyen Nzangola da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar.

Source: Twitter
Maharan sun shiga garin da babura
Rahotan jaridar Daily Trust ya ce maharan sun kai harin ne tsakanin ƙarfe 5 zuwa 6 na yammacin Lahadi, 13 ga watan Satumban 2026.
An ce sun shiga cikin garin ne a kan babura, inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa. Hakan ya tilasta wa mazauna yankin tserewa daga gidajensu domin kuɓutar da rayukansu.
Shugaban karamar hukumar Hong ya tabbatar da harin
Shugaban ƙaramar hukumar Hong, Hon. Aliyu Sa’ad Yerima Hong, ya tabbatar da faruwar lamarin
Hon. Aliyu ya ziyarci al’ummar da lamarin ya shafa, inda ya jajanta wa iyalan mutanen da aka kashe.
Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnati na ƙoƙarin inganta tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, The Punch ta kawo labarin.
An buƙaci mazauna su taimaka wa jami’an tsaro
Sai dai shugaban karamar hukumar a buƙaci mazauna yankin da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani motsi na mutanen da ake zargi da aikata laifuka.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
Ya kuma yi kira ga al’umma da su fallasa masu leƙen asiri ko waɗanda ke taimaka wa ’yan ta’adda a cikinsu.
Ya gargaɗi cewa duk wanda aka samu yana ɓoye masu aikata laifi, haɗa kai da ’yan ta’adda ko lalata zaman lafiyar al’umma, zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Jama'a sun nemi ƙarin matakan tsaro
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Adamawa da su gaggauta ƙara yawan matakan tsaro a yankin.
Sun ce hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen barazanar hare-haren ’yan ta’adda tare da kare mazauna karkara daga ci gaba da fuskantar irin waɗannan hare-hare.

Source: Original
Sabon kwamandan da zai jagoranci yakin Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar sojojin Najeriya ta naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci ayyukan sojoji kan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.
Sabon kwamandan, Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, ya maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, wanda shi ne kwamanda na 15 na Operation Hadin Kai.
Asali: Legit.ng
