"Ku Shirya," NiMet Ta Yi Hasashen Abubuwan da Za su Faru a cikin Kwanaki 3 a Najeriya

"Ku Shirya," NiMet Ta Yi Hasashen Abubuwan da Za su Faru a cikin Kwanaki 3 a Najeriya

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da hasken rana a sassan Najeriya daga yau Litinin zuwa ranar Laraba
  • Hukumar ta ce ana sa ran tsawa da ruwan sama a wasu jihohin Arewa da kudancin ƙasar nan
  • NiMet ta yi gargaɗin cewa iska mai ƙarfi na iya yin gaba kafin zuwan ruwan sama a wuraren da ake sa ran tsawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen ruwan sama da hasken rana a sassan ƙasar daga Litinin zuwa Laraba.

A cikin hasashen yanayin da hukumar ta fitar ranar Lahadi a Abuja, NiMet ta ce ana sa ran samun sararin samaniya mai hasken rana a yankin Arewa ranar Litinin, tare da wasu 'yan gizagizai a sassan yankin.

Kara karanta wannan

Babbar dama: Gwamnatin tarayya za ta 'ɗauki' yan Najeriya miliyan 2 aiki, an ji yadda tsarin yake

Ruwan sama.
Ruwan sama da sauka da tsawa a wasu sassan Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta ce hukumar ta kuma yi hasashen tsawa lokaci-lokaci tare da ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici a wasu sassan jihar Taraba da rana da yamma.

Hasashen yanayin ranar Litinin

NiMet ta ce ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun tazarar hasken rana a yankin Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.

A yankin Kudu kuwa, ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun hasken rana, yayin da ake hasashen yiwuwar tsawa da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Rivers, Bayelsa, Akwa Ibom da Cross River.

Hukumar ta kuma lissafa Oyo, Osun, Ondo, Lagos, Edo, Delta, Imo, Abia, Ebonyi, Anambra, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom cikin jihohin da ake sa ran samun ruwan sama.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

NiMet ta yi hasashen gobe Talata

A ranar Talata, NiMet ta yi hasashen sararin samaniya mai hasken rana tare da wasu 'yan gizagizai a dukkan yankin Arewa, yayin da ake sa ran tsawa lokaci-lokaci da ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici a wasu sassan Taraba.

A cewar NiMet, ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun tazarar hasken rana a yankin Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.

Haka kuma, ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun tazarar hasken rana a yankin Kudu.

Hukumar ta yi hasashen tsawa tare da ruwan sama matsakaici a wasu sassan Ondo, Osun, Ogun, Lagos, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Bayelsa, Edo da Delta daga baya da rana.

Kara karanta wannan

Karin kudin fetur babu makawa yayin da ake wayyo lita ta haura N1300

NiMet.
Hedkwatar hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) da ke Abuja Hoto: @NiMet
Source: Twitter

Hasashen ranar Laraba

Hukumar ta yi hasashen sararin samaniya mai hasken rana tare da wasu 'yan gizagizai a dukkan yankin Arewa ranar Laraba.

A cewar NiMet, ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun tazarar hasken rana a yankin Arewa ta Tsakiya.

A yankin Kudu kuwa, ana sa ran yanayi mai cike da gizagizai tare da samun tazarar hasken rana, yayin da ake sa ran tsawa tare da ruwan sama matsakaici a wasu sassan Delta, Edo, Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom da Rivers.

NiMet ta yi hasashen ruwan sama

Kun ji cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa watau NiMet ta fitar da sanarwa game da yankunan da za a samu ruwan sama a Najeriya.

A hasashen da NiMet ta yi, ta sanar da cewa za a yi ruwan sama a jihohi da dama a Arewacin Najeriya ciki har da Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262