Siyasar Kano: NNPP Ta Goyi Bayan Ganawar Ganduje, Kawu Sumaila da Sauransu
- Tsagin jam’iyyar NNPP a Kano ta ce shugabannin jam’iyya su san da taron da wasu 'yan majalisar tarayya suka yi da shugaban APC
- Shugaban tsagin na NNPP, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, ya ce manufar taron ita ce tattaunawa kan ci gaban yankunan jihar Kano
- Ya ce ba wata maganar sauya sheka da ke tattare da lamarin, kuma zance ake na hadin gwiwa, ba abin da ya shafi mutum daya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban tsagin NNPP a jihar Kano ya kare wasu yan jam'iyyar da suka gana da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, a wani taro da ya tayar da kura a fagen siyasa.
Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Hon. Kabiru Alhassan mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure sun halarci taron.

Asali: Facebook
Leadership ta wallafa cewa Hon. Aliyu Sani Madaki mai wakiltar Dala da tsohon dan majalisa, Hon. Badamasi Ayuba ma sun shaida taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron a aka gudanar da shi a Abuja ya jawo maganganu da dama musamman dangane da yiwuwar sauya sheka kafin zaben 2027.
'Ba taron sauya sheka ba ne,' NNPP
A yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Laraba, shugaban tsagin NNPP a jihar Kano, Mas’ud El-Jibrin Doguwa, ya ce taron ya gudana ne da yardar shugabannin jam’iyya.
Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce manufar taron ita ce tattaunawa kan hanyoyin samar da ci gaba a mazabun 'yan majalisar.
Ya bayyana cewa siyasa ba wai kawai adawa ba ce, har da hadin kai da fahimtar juna, yana mai cewa dole ne wakilai su tattauna da kowane bangare domin ciyar da al’umma gaba.
Doguwa ya ce:
“Tattaunawa da shugaban APC na kasa wani bangare ne na bincike don gano jam’iyyar da za ta iya kawo wa yankunan su sauyi da ayyuka.”
Ayyukan da 'yan jam'iyyar NNPP suka yi
Jagora a jam’iyyar ya kara da cewa wakilan NNPP kamar Kawu Sumaila da sauran su sun aiwatar da ayyuka na kimanin Naira biliyan 90 a mazabunsu.
A cewarsa:
“A karshe, wakilan za su nemi shawarar shugabannin jam’iyya kafin yanke hukunci kan yiwuwar kawance ko sauya sheka.
Hukuncin kotu game da dan NNPP
Doguwa ya yi karin haske kan hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar Talata kan Barista Dalhatu, wani dan NNPP, yana mai cewa hukuncin ya shafe shi a matsayin mutum, ba NNPP ba.
Ya ce jam’iyyar ba ta da hannu a karar da aka shigar da hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano, kuma ya jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kare mutuncinta da bin doka.
Ganduje ya ce Kwankwaso zai koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce nan kusa Sanata Rabiu Kwankwaso zai koma APC.
Ganduje ya ce a yanzu haka jam'iyyar NNPP ta mutu murus, saboda haka Kwankwaso ba shi da mafita illa ya shiga APC.
Abdullahi Ganduje ya ce za su yi maraba da Kwankwaso idan ya sauya sheka domin dama shi dan asalin jam'iyyar APC ne a karon farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng