Gawuna Ya Yi Matsaya tsakanin Shiga APC da Zama a NDC tare da Kwankwaso
- Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a 2023, Nasir Gawuna, ya ƙi komawa jam’iyyar APC duk da komawar wasu manyan mutanensa
- Gawuna ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar NDC tare da Rabiu Kwankwaso, inda aka ce an ba shi tikitin takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya
- Wani na kusa da Gawuna, Badaru Umar, ya bayyana cewa sun yi ƙoƙarin shawo kan sa ya koma APC, amma ya nace kan ci gaba da zama a NDC gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, Nasir Gawuna, ya yi watsi da yunkurin da ake yi na ganin ya koma jam’iyyar APC daga NDC.

Kara karanta wannan
Pantami ya ce ba ya fargabar cin zaben 2027, ya fadi irin mulkin da zai yi a Gombe
Matakin nasa ya biyo bayan komawar wasu daga cikin manyan mutanensa da magoya bayansa APC, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa shi ma zai koma jam’iyyar mai mulki.

Source: Twitter
Premium Times ta ruwaito cewa Badaru Umar, wani na kusa da Gawuna kuma tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo, ya bayyana cewa Gawuna ya nace kan ci gaba da kasancewa a NDC.
Mutanen Gawuna sun koma APC
A ranar 1 ga Satumba, Badaru Umar ya jagoranci tawagar wasu daga cikin manyan abokan siyasar Gawuna zuwa wata ganawa da Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da Mataimakinsa, Murtala Garo.
Tawagar ta haɗa da Ali Datti-Yako, mataimakin shugaban NDC na jihar Kano, Uba Danzainab, Aminu Faruk, Sani Jibrin, Salisu Muhammad, Musa Indabo, Muhammad Bala, Hassan Abdullahi da Abdurrahman Muhammad.
Daga bisani, waɗannan ’yan siyasa tare da wasu daga cikin magoya bayansu sun koma APC a hukumance a ranar 5 ga Satumba.
Badaru ya fadi dalilin shiga APC
Da yake magana a ranar Litinin, Badaru Umar ya ce sun koma APC ne domin su samu damar mara wa shirye-shiryen ci gaban gwamnatin Gwamna Abba Yusuf baya.
Ya ce:
“Mun koma APC ne saboda mun yi imanin cewa ita ce dandalin da ya dace domin cimma manufofinmu na siyasa.
“Da farko mun jagoranci Gawuna zuwa ADC, daga baya NDC, da nufin kawai ganin ya samu tikitin takarar gwamna, amma hakan bai samu ba.
“Yayin da muka yanke shawarar komawa APC, Gawuna ya dage kan ci gaba da kasancewa a NDC, inda aka ba shi tikitin takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.”

Source: Twitter
Maganar takarar gwamna a Kano
A hirar da Lumana Radiyo ya wallafa a Facebook, Badaru ya ƙara bayyana cewa duk da rashin samun tikitin takarar gwamna, sun kasa shawo kan Gawuna ya koma APC.
Ya ce hakan ya sa komawar tsohon mataimakin gwamnan Kano APC ke ƙara zama abu mai wahala, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
An kama dan sandan bogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai shekaru 35 bisa zargin yin karyar shi jami'in tsaro ne.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce an kama Adamu Musa ne a unguwar Kureken Sani da ke Kano.
Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana gabatar da kansa a matsayin babban jami’i mai tasiri wajen ɗaukar ’yan sanda aiki da sauya wuraren aiki domin ya damfari jama’a.
Asali: Legit.ng

