Ana Jita Jitar Zuwan Kwankwaso APC, Shugabanta Ya Gindaya Sharuɗa a Kano

Ana Jita Jitar Zuwan Kwankwaso APC, Shugabanta Ya Gindaya Sharuɗa a Kano

  • Shugaban APC Kano, Abdullahi Abbas ya ce kofar jam’iyyar APC a bude take ga kowa, musamman ga masu kishin kasa da ci gaba
  • Abbas ya bayyana cewa suna da labarin wasu jiga-jigan NNPP da aka kora na shirin sauya sheka zuwa APC domin tsira daga matsaloli
  • Ya ce jam’iyyar ta umarci ofisoshinta da su fara karbar sunayen masu sha’awar shiga, tare da tabbatar da ikon shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi magana kan musu sha'awar shiga cikinta.

Abbas ya ce jam'iyyar APC ta kowa da kowa ce musamman ga masu son kawo ci gaba a kasa.

APC ta gargadi masu shirin shigowa cikinta
Jam'iyyar APC a Kano tana maraba da Kwankwaso da sauran masu son shiga cikinta. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

APC ta magantu kan rade-radin sauya shekar Kwankwaso

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Faizu Alfindiki ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Abbas ya ce suna da labarin wasu na son shiga jam'iyyar saboda sun aikata badakala a kasa.

A cewarsa:

"Muna da labarin jagoran jam'iyyar NNPP da wadanda aka kora suna shirye-shirye ko sha'awar shigawo jam'iyyarmu ta APC mai daraja.
"Wannan abu ne mai kyau kuma muna murna da farin ciki da wannan tsari kuma dama shi ne tsarin da jam'iyyar da shugaban kasa suka bayar.
"Tsarin shi ne duk mai son shigowa jam'iyyar a buda masa ya shigo cikinta kamar yadda tsarin dokar jam'iyyar ya shimfida."

Shugaban APC ya tabbatar da cewa kofar APC a bude ta ke ga kowa inda ya umarci ofisoshin jam'iyyar su fara daukar sunayensu.

Abbas ya kuma ba shugabannin jam'iyyar tabbacin cewa sune ke jagorancinta kuma za su ci gaba da rike madafun iko har zuwa lokacin karewar wa'adinsu.

Ya kara da cewa:

"Ina son amfani da wannan dama da cewa duk masu son shigowa jam'iyyar kofa a bude take kuma tuni muka umarci ofisoshinmu su fara daukar sunayen masu sha'awa.

"Haka duk mai sha'awarar neman takara ko ta mulki ko jam'iyya kullum a shirye muke saboda babu dan mowa ko gora."
APC a Kano tana maraba da Kwankwaso da masu son shiga cikinta
Jam'iyyar APC ta ce kofofinta a bude suke ga Kwankwaso da masu sha'awar shigowa. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Gargadin APC ga masu shirin shigowa a Kano

Abbas ya gargadi masu sha'awar shigowa jam'iyyar da cewa duk wanda ya san yana da laifi na cin hanci to APC ba tudun na tsira ba ce a gare shi.

"Haka kuma muna da labarin wasu suna son shigowa jam'iyyarmu saboda buƙatar kansu.
"Ko saboda sun bata sunansu ko siyasarsu a kasa ko kuma a jihar Kano ko an kama su da badakala saboda EFCC da ICPC na nemansu.
"Saboda suna tsammanin za su samu sassauci a jam'iyyarmu to muna son fada musu APC ba tudun na tsira ba ce."

- Cewar Abdullahi Abbas

Ganduje ya sha alwashi kan zaben 2027

Kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC a Najeriya, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar na ƙoƙarin samun ƙarin jihohi fiye da guda 21.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa APC za ta iya cimma hakan ta hanyar haɗin gwiwar siyasa ko kuma ta ta nasarar zaɓe a sauran jihohi.

Ganduje ya ce ko da suna da iko kan jihohi 21, amma suna hangen wasu jihohi su shigo musu ta hanyoyi daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.