Hukumar yan sandan NAjeriya
Jami'an 'yan sanda a jihar Bauchi ta kama wata matar aure, Khadija Adamu da ta hallaka 'yar kishiyarta mai shekaru biyar saboda ta bata jikinta da kashi.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci jami'an tsaro da su fatattaki 'yan bola jari da masu baban bola shiga yankunan Mabushi da Katampe a birnin.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya kaddamar da rabon kayan abinci ga marasa karfi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar, za a raba buhunan abinci 387,200.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kuɓutar da mutane 171 da aka yi garkuwa da su a faɗin jihar cikin watanni huɗu.
Masu garkuwa sun sace malamin addinin Musulunci, Alfa Fasasi da wasu yayin raka gawa zuwa makabarta a jihar Kogi, 'yan bindigan sun shammace su ne kan hanyar Lokoja.
Wani dan achaba mai suna Yahuza ya rasa ransa bayan fasinjansa ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba a yankin Nyanya da babban birnin tarayya da Abuja.
Yan sanda sun yi nasarar kame wasu tsagerun 'yan bindigan da ake zargin sun sace wasu mutane tare da hallaka wasu dama a yankin Zaria da ke Kaduna.
Kotun da ke sauraron ƙarar ɗan sandan da ya halaka lauya a jihar Legas ta zartar da hukuncinta. Kotun ta yanke hukuncin kisan ne bayan ta same shi da laifi.
Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da masu daukar doka a hannunsu kan zargin satar mazakuta a birnin Tarayya Abuja, ya ce wannan sharri ne kawai na matsafa.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari