Masu Garkuwa Sun Yi Awun Gaba Da Masu Rakiyar Gawa Zuwa Makabarta A Jihar Kogi

Masu Garkuwa Sun Yi Awun Gaba Da Masu Rakiyar Gawa Zuwa Makabarta A Jihar Kogi

  • 'Yan bindiga sun yi awun gaba da wani malamin addinin Musulunci yayin da su ke raka gawa zuwa makabarta
  • Malamin mai suna Alfa Fasasi Ola ya gamu da tsautsayin ne tare da wasu jama'a yayin rakiyar gawar daga Lokoja zuwa karamar hukumar Ijumu
  • Maharan daga bisani sun kira wayar iyalan wadanda aka kaman tare da bukatar kudin fansa Naira miliyan 10

Jihar Kogi - Masu garkuwa sun sace malamin addinin Musulunci, Alfa Fasasi Ola da dan uwansa yayin da su ke raka gawa makabarta a jihar Kogi.

Malamin da sauran mutanen na raka gawar wani babban limami ne mai suna Sheikh Musa Olorunkemi daga Lokoja zuwa karamar hukumar Ijumu.

'Yan bindiga sun sace malamin Musulunci da wasu mutane a jihar Kogi
'Yan bindiga sun addabi Arewa maso Tsakiyar Najeriya. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Me ya faru lokacin sace malamin a Kogi?

Wani da ya sha da kyar ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a Oshokoshoko da ke kan hanyar Lokoja zuwa Obajana da Kabba, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce motar tasu na gaba da wacce ta dauki gawar Sheikh Musa wanda ya rasu a ranar Lahadi 8 ga watan Oktoba.

Wata majiya ta tabbatar da cewa lambobin wayar wadanda aka kaman a kashe su ke tun bayan yin garkuwa da aka yi da su.

Wane martani hukumomi su ka yi kan sace malamin?

Majiyar ta tabbatar da cewa maharan sun kira iyalan wadanda su ka kaman tare da neman kudin fansa har Naira miliyan 10 don sake su.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ya ci tura bayan rashin daga waya da ya yi yayin da aka kira shi, cewar PM News.

Har ila yau, hadimin gwamnan jihar kan harkokin tsaro, Jerry Omadora ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro su na yin duk mai yiyuwa don kwato wadanda aka sacen.

Kara karanta wannan

'Yan Bindga 67 Sun Baƙunci Lahira Yayin da Jami'ai Suka Ceto Mutane 20 da Aka Yi Garkuwa da Su a Bauchi

Mutane da dama sun mutu yayin rikicin manoma da makiyaya a Kogi

A wani labarin, Mutane da dama sun mutu yayin rikici tsakanin manoma da makiyaya a garin Isanlu da ke karamar hukumar Yagba a jihar Kogi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rikicin ya faru ne bayan wasu mahara sun kai farmaki kan wani manomi a hanyarshi ta zuwa gona.

Arewa maso Tsakiya na fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya musamman a yankunan karkara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel