Bayan Dokar Ƙayyade Iyali, Vietnam ta Lashe Amanta, Ta Ce a Ci Gaba da Haihuwa
- Ƙasar Vietnam ta fara ba iyaye tallafi, karin hutun haihuwa da wasu alawus bayan soke dokar iyakance haihuwar
- Gwamnati na fargabar karancin matasa masu aiki yayin da yawan tsofaffi ke karuwa, amma iyalai da dama sun ce tsadar rayuwa na hana su kara haihuwa
- Masana sun ce tallafin kudi kadai ba zai wadatar ba, suna bukatar gwamnati ta samar da cikakken tallafi kan gidaje, kula da yara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Vietnam - Shekara guda bayan Vietnam ta soke dokar da ta takaita iyalai ga yara biyu, an sake sauya tsari a kasar.
Gwamnati ta fara aiwatar da sabuwar dokar kara haihuwa daga ranar Laraba 1 ga watan Yulin 2026.

Source: Getty Images
Abin da sabuwar dokar ke kunshe da ita
Sabuwar dokar ta kara hutun haihuwa daga watanni shida zuwa bakwai ga mata masu haihuwar yaro na biyu, tare da tallafin gwaje-gwajen ciki da na jarirai, cewar France 24.
Har ila yau, wasu iyaye mata da suka cika sharudda za su samu tallafin kudi sau daya har dala 228, kwatankwacin kusan kashi biyu bisa uku na matsakaicin albashin wata.
Nguyen Kim Bich mai shekara 32 ta ce idan ta haifi yaro na biyu za ta samu karin hutun haihuwa, karin kwanakin hutun mijinta da tallafin gwaje-gwajen lafiya.
Sai dai ta bayyana cewa wannan tallafi bai isa ya sa su kara haihuwa ba, saboda kusan rabin kudin shigar iyalinsu na wata yana karewa wajen kula da ɗansu.
Shugabar bangaren yawan jama'a da ci gaba ta Asusun Majalisar Dinkin Duniya kan Yawan Jama'a, Pham Thi Lan, ta ce wannan babbar sauyi ce.
Ta bayyana cewa Vietnam ta sauya daga manufar takaita haihuwa zuwa manufar bunkasa yawan jama'a domin tinkarar matsalolin da ke tafe.

Source: Getty Images
Abin da ke jawo yawan tsofaffi a Vietnam
A baya, jami'an jam'iyyar kwaminis suna fuskantar hukunci idan suka haifi yaro na uku, amma an soke wannan tsarin a bara.
Yanzu kasar Vietnam na daga cikin kasashen da yawan tsofaffi ke karuwa cikin sauri saboda raguwar haihuwa da kuma karuwar tsawon rayuwa.
Masana tattalin arziki sun gargadi cewa hakan na iya haifar da karancin ma'aikata tare da kara nauyi kan tsarin kula da tsofaffi nan gaba.
Yawan haihuwa a Vietnam ya ragu zuwa yara 1.93 ga kowace mace, kasa da adadin 2.1 da ake bukata domin daidaita yawan jama'a, cewar The Guardian.
Duk da cewa tattalin arzikin Vietnam na bunkasa cikin sauri a Asiya, kasar har yanzu ba ta kai matsayin kasashe masu arziki ba.
Bankin Duniya ya gargadi cewa Vietnam na da karamin lokaci kawai domin yin gyare-gyare kafin tsufar al'umma ta janyo raguwar ci gaban tattalin arziki.
Pham Thi Lan ta ce tallafin lokaci guda kamar kyautar kudi ba ya wadatar, domin iyalai na bukatar ci gaba da samun tallafi wajen renon yara.
An ƙaddamar shirin rage haihuwa a Najeriya
A baya, an ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata shiri na samar da hanyoyin bada tazarar haihuwa na zamani a Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce an kaddamar da shirin ne domin inganta rayuwar yan Najeriya, wanda hakan na cikin ababen da gwamnatin ke son cimmawa.
Tuni dai an kafa wata kwamiti ta musamman da zai saka ido kan yawan al'umma a Najeriya da Shugaba Buhari da kansa zai shugabanta.
Asali: Legit.ng

