Gwamnati Ta Fadi Abin da zai Gudana a Taron Cika Shekara 1 da Rasuwar Buhari
- Gwamnatin tarayya ta fara shirin tuna wa da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayin da ake shirin cka shekara daya da rasuwarsa
- Daga cikin abubuwan da aka tsara, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da littafin ta'aziyya domin tunawa da marigayi Muhammadu Buhari
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya fadi yadda aka tsara gudanar da addu'o'in haɗin gwiwa na addinai domin yi wa Buhari addu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai ƙaddamar da wani littafi mai ɗauke da saƙonnin ta'aziyya da karramawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a wani taron tunawa da cikar shekara ɗaya da rasuwarsa.
Shugaban kwamitin shirya taron tunawa da marigayin na ƙasa baki ɗaya, kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2026.

Source: Twitter
Arise News ta kawo labarin cewa Boss Mustapha ya ce an tsara taron ne domin tunawa da rayuwar Buhari da kuma gudunmawar da ya bayar wajen hidimtawa Najeriya.
Ana shirin tuna wa da Buhari
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Boss Mustapha ya bayyana cewa taron zai haɗa iyalan marigayin, abokansa, waɗanda suka yi aiki tare da shi, jami'an gwamnati da sauran masu yi masa fatan alheri domin yi masa addu'a.
A cewarsa, babban abin da taron zai ƙunsa shi ne addu'o'in haɗin gwiwa na mabiya addinai daban-daban, domin nuna ƙimar haɗin kai, imani da zaman lafiya da Buhari ya tsaya a kai a lokacin rayuwarsa da shugabancinsa.
Ya ƙara da cewa wasu zaɓaɓɓun mutane da suka yi aiki tare da marigayin za su gabatar da jawabai kan irin tarihin da ya bari da kuma abubuwan da suka gani a zamansu tare da shi.

Source: Facebook
Boss Mustapha ya ce:
"Shugaban ƙasa, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a matsayinsa na babban baƙon girmamawa, zai ƙaddamar da littafin ta'aziyyada girmama Muhammadu Buhari."
Yadda ake shirin karrama Buhari
Tsohon SGF ya bayyana cewa littafin ya tattaro saƙonnin ta'aziyya daga shugabannin ƙasashe, jami'an diflomasiyya da fitattun jagororin siyasa daga sassa daban-daban na duniya.
Ya ce:
"A cikin shafukan littafin, al'ummar duniya, ciki har da shugabannin ƙasashe, jami'an diflomasiyya da jagororin siyasa, sun tuna marigayi shugaban ƙasar a matsayin mutum mai sauƙin kai, juriya da riƙon amana."
Ya ƙara da cewa:
"Bayan rasuwarsa yana da shekara 82 a ranar 13 ga Yulin bara, duniya ta girmama rayuwarsa saboda tawali'unsa da kuma kasancewarsa abin koyi. Ina kuma ƙara jaddada cewa ba za a sayar da littafin ba, kuma ba a wallafa shi domin tara kuɗi ba. Za a raba shi kyauta."
Yadda aka kalubalanci gwamnatin Buhari
A baya, kun samu labarin cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana takun-saka da aka yi da shi lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari, inda ya tsaya kai da fata wajen daidaita ayyuka.
Bukola Saraki ya ce ya kalubalanci gwamnatin a wancan lokaci kan buƙatun rancen ƙasashen waje da Majalisar Dattawa ta nace sai an tantance domin hana karbo bashi barkatai a Najeriya.
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya bukaci ƙarfafa gaskiya, ingantattun cibiyoyi, cinikayya, ilimi da kirkire-kirkire domin samun ci gaba mai ɗorewa wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar yan kasa.
Asali: Legit.ng


