Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Mata Kan Zargin Watsa Wa Mijinta Tafasasshen Man Gyada a Ribas

Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Mata Kan Zargin Watsa Wa Mijinta Tafasasshen Man Gyada a Ribas

  • Asirin wata mata ya tonu bayan ta watsa wa mijinta tafasasshen man gyada a jikinsa
  • Matar mai suna Hope ta yi wa mijin nata Nwanko wanka da man gyadan ne saboda wata 'yar hayaniya
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba

Jihar Ribas - Rundunar 'yan sanda a jihar Ribas ta sanar da cafke matar da ta yi wa mijinta wanka da tafasasshen man gyada a jihar.

Matar mai suna Hope Nwala ana zargin ta da watsawa mijinta, Ekelediri Nwanko man gyada kan wata karamar jayayya, cewar Punch.

'Yan sanda sun kama matar da ta yi wa mijinta wanka da tafasasshen man gyada
Yan sanda sun kama matar bayan ta tsere. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Me ake zargin matar da aikatawa a Ribas?

Nwala ta aikata laifin ne a kauyen Okehi da ke karamar hukumar Etche a jihar bayan mijin ya kwanta bacci.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce matar na hannun jami'ansu, Newstral ta tattaro.

Grace ta ce jami'ansu sun yi nasarar kama matar ce bayan ta tsere ganin girman laifin da ta aikata.

Ta ce:

"An kama matar kuma ta na hannun jami'anmu, an cafke ta ne a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba.
"A yanzu haka ana kan bincike wanda da zarar an kammala za a dauki matakin da ya dace."

Meye mijin matar da ake zargi ya ce?

Ana zargin matar aikata hakan ne bayan mijin nata ya tinkare ta da zargin cewa wani na zuwa wurinta da kanwarta.

Mijin matar ya ce ta fara sauya halayenta tun bayan dawowar kanwarta gidan a 'yan kwanakin nan, Nairaland ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Kashe 'Yar Kishiyarta Kan Bata Jikinta Da Kashi, Ta Yi Martani

Nwanko ya kara da cewa hakan ya tilasta shi sallamar kanwar tata inda abin bai mata dadi ba wanda ya jawo musu cece-kuce.

'Yan sanda sun cafke matar da ta yi ajalin 'yar kishiyarta

A wani labarin, jami'an 'yan sanda sun cafke matar da ta hallaka 'yar kishiyarta bayan ta yi kashi a jikinta.

Matar mai suna Khadija Adamu ta roki yafiya a wurin hukumomi inda ta ce iyayen yarinyar sun yafe mata.

Matar ta bayyana cewa ba da gangan ta aikata kisan ba tun da daman yarinyar ta saba yin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel