Yan Sanda Sun Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Sace Mazakutar Wani Mutum a Bauchi

Yan Sanda Sun Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Sace Mazakutar Wani Mutum a Bauchi

  • Jami'an yan sanda a jihar Bauchi sun damke wasu mutane uku da ake zargi da sace mazakutar wani
  • Biyu daga cikin wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka ce sun mikawa ogansu mazakutar
  • Sai dai, Yonana Abubakar wanda ke da ikon mayarwa mutumin da mazakutarsa ya mutu kafin ya kai ga mayar da shi

Jihar Bauchi - Wani matashi dan shekaru 30 mai suna Joshua Yonana, ya bayyana yadda suke sace mazakutar maza, cewa suna amfani shafa asiri a hannayensu don sace mazakutar.

Wanda ake zargin ya ce ya yi amfani da maganin wajen sace mazakutar wani mutum mai suna Usman Sale a yankin Sabon Garin Nabardo, a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto.

Yan sanda sun kama masu satar mazakuta a Bauchi
Yan Sanda Sun Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Sace Mazakutar Wani Mutum Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda muka sace mazakutar Usman Sale, wadanda ake zargi

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

An gurfanar da Yonana tare da wani abokin ta'asarsa a hedkwatar rundunar yan sanda ta jihar Bauchi a ranar Talata, inda ya sanar da manema labarai cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da gaske ne cewa na sace mazakutar wani mutum. Mun shafa magani a hannayenmu sannan duk wanda muka sha hannu da shi, zai rasa mazakutarsa.
"Na sha hannu da wanda abun ya rits ada shi a Nabardo sannan na sace mazakutarsa. Lokacin da na sace mazakutar, na mikawa abokin harkata, Bitrus wanda shi kuma ya kai wa ubangidanmu, Yonana Abubakar.
"Ban san abun da ubangidanmu ke yi da shi ba saboda wannan shine karo na farko da nake yin irin wannan abu. Basu fada mani nawa za su biyani a kan ko wani mazakuta ba kuma wannan ne karo na farko da nake yi kuma mazakuta daya kawai na sace. Abun takaici shine yanzu wanda ke da ikon mayarwa ya mutu."

Kara karanta wannan

Hotunan Wike a Gidan Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Na Tsagin Atiku, Bayanai Sun Fito

Yonana wanda ya kasance manomi da mata da yara hudu ya kara da cewar:

"Ba zan ji dadi ba idan aka sace mun mazakuta na kuma na yi danasanin shiga wannan mugun abu sannan ina so gwamnati ta yafe mani.
"Eh, idan aka sace mazakutar namiji, oganmu yana da asirin mayarwa mai shi da shi amma a kan Nabardo, mutumin ya mutu kuma ba mu san yadda ake mayar da mazakutar ba. Mazakutar da aka sace yana hannun oganmu da ya mutu."

Da yake martani, abokin harkallarsa Bitrus Iliya mai shekaru 27 ya ce:

"Da gaske ne cewa abokin aikina Joshua Yonana ya sace mazakutar wani mutum kuma ya bani. Yana bani mazakutar, na tura shi ga oganmu, Yonana Abubakar.
"Maganar gaskiya, oganmu bai nuna mana abun da zai yi da shi ba kuma bai fada mana nawa zai ba mu kan kowani daya ba amma dai ya yi alkawarin bamu kudi idan ya kammala abun da yake niyan yi da shi. Mun fara aikin a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Yanzu: "Na Yi Amfani Da Sadiq Abubakar Yayin Rubuta WAEC": Atiku Ya Yi Martani Kan Zargin Satifiket Din Bogi

"Shugabanmu ne yake da asirin sacewa da dawo da mazakutar mutum kuma kafin ya mutu, ya fada ma jami'an tsaro cewa ya karbi mazakutar mutumin a Nabardo.
"Kafin mutuwarsa, oganmu ya yarda zai mayarwa mutumin kuma a cikin haka, ya yi kokarin guduwa sai daya daga cikin maharban ya harbe shi da bindiga sannan ya fadi. Ogabmu ya ba da lokaci, 8:00 na dare zai mayar da mazakutar amma ya mutu kafin lokacin."

Rundunar yan sanda ta yi martani

A na shi bangaren, kwamishinan yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya ce:

"A ranar 28 ga watan Satumba, rundunar ta samu bayanai daga wata majiya abun dogaro cewa wasu kwararrun maharba masu suna, Muhammad Umar na kauyen Takanda da Hussain Umar na kauyen Zaranda sun kama wasu mutane, Joshua Yonana, Bitrus Iliya, da Yonana Abubakar, duk a kauyen Waya kan sace sassan jiki."

CP Muhammad ya ce binciken da maharban suka yi ya yi sanadiyar yi wa wadanda ake zargin duka a kokarinsu na tilasta su fadin gaskiya kan zargin da ake masu.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Sama da Mutum 170 da Aka Sace a Jihar Arewa

"Nan take daya daga cikin wadanda ake zargin, Yonana Abubakar, ya fadi sannan aka kai shi asibiti mafi kusa kuma daga baya ya mutu.
"Da samun rahoton, wata tawagar jami'an tsaro karkashin jagorancin DPO na Toro suka shiga aiki, suka isa wajen sannan suka kama maharban yayin da aka bai yan uwan mamacin gawarsa don su binne.
"Binciken farko ya nuna cewa mutum uku da aka kama ana arginsu da sace mazakutar wani Usman Sale a Sabon Garin Nabardo."

Yayin bincike, wadanda ake zargin sun tona cewa sun aikata laifin da ake zarginsu wanda ya yi sanadiyar kama ogansu, wanda ya mutu yayin bincike.

Ana nan ana ci gaba da bincike, inda daga nan za a kai wadanda ake zargin kotu don yanke masu hukunci, rahoton Leadership.

Matasa sun kashe dan achaba kan zargin satar mazakuta a Abuja

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wasu fusatattun matasa sun kai wa wani dan achaba da ake zargi da satar mazakuta hari a yankin Nyanya da ke Abuja.

An kwaci dan achaban a hannunsu inda aka kai shi asibiti, amma daga baya ya ce ga garinku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel