Ministan Abuja, Nyesom Wike Ya Umarci Hana ’Yan Bola Jari Shiga Yankin Mabushi Da Katampe

Ministan Abuja, Nyesom Wike Ya Umarci Hana ’Yan Bola Jari Shiga Yankin Mabushi Da Katampe

  • Minista Nyesom Wike ya umarci jami’an tsaro da su dakile 'yan bola jari shiga yankin Mabushi da Katampe
  • Wike ya ba da wannan gargadi ne yayin da matasa ‘yan bola jari da makanikai da sauransu ke damun wuraren
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yankunan na fama da matsalar rashin tsaro wanda shi ne dalilin daukar matakin

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci jami’an tsaro da su hana masu baban bola da makanikai shiga yankin Mabushi da Katampe na birnin Abuja.

Wike ya bayyana haka ne a yau Talata 10 ga watan Oktoba inda ya ce mutane na amfani da wadannan wuraren don aikata laifuka, The Nation ta tattaro.

Wike ya umarci jami'an tsaro su dakile 'yan bola jari zuwa yakin Mabushi
Nyesom Wike Ya Umarci Hana ’Yan Bola Jari Shiga Abuja. Hoto: Nyeson Wike, FCTA.
Asali: Facebook

Meye Wike ke cewa kan tsaron Abuja?

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bola jari da makanikai da kafintoci na daga cikin wadanda ke kawo matsala a yankin na Mabushi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Za mu yi duk mai yiyuwa don ganin mun rage yawan aikata laifuka a yankunan kuma ba za mu bar wadannan mutane su ci gaba da haka ba.
“Saboda wannan abin ya yi muni yanzu dole ku tabbatar kun kawo karshen hakan cikin kankanin lokaci.”

Wane mataki aka dauka kan samar da tsaro a Abuja?

Wike ya ce abin takaici ne abubuwan da su ke faruwa don haka babu wani ba da wa’adi kawai ku tabbatar kun watsar da su a wurin.

Yayin da ya ke martani kan wannan lamari, Kwadineton gudanar da birnin Abuja, Mukhtar Galadima ya ce abin yanzu ya yi yawa a yankunan.

Galadima ya koka kan yadda hanyoyin yankunan su ka dawo matattarar ‘yan bola da masu tsine-tsine musamman a yankunana Mabushi da Katampe.

Ya ce:

“Duba da yadda abubuwa ke faruwa yanzu musamman rashin tsaro da ya mamayi kasar baki daya, yin amfani da wuraren a wannan lokaci bai dace ba ko kadan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindga 67 Sun Baƙunci Lahira Yayin da Jami'ai Suka Ceto Mutane 20 da Aka Yi Garkuwa da Su a Bauchi

An kama wasu matasa da ke jawo hayaniya kusa da gidan Wike

A wani labarin, Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike ya ba da umarnin kama wasu matasa guda uku da ke kawo hayaniya kusa da gidansa a cikin birnin.

Jami’an tsaro sun cafke matasan ne bayan musu gargadin a lokuta da dama inda su ka bukaci matasan su guji ci gaba da kawo hayaniya a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel