Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Yi Wa Abokinsa Fashin N2.9m a Kano

Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Yi Wa Abokinsa Fashin N2.9m a Kano

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Kano sun cafke matasa uku kan zargin fashi da makami a jihar
  • Wanda ake zargi Yusuf Sunusi ya hada baki da wasu mutane biyu don yin fashi ga abokinsa, Nura Ibrahim
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Laraba 11 ga watan Oktoba

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kama wani matashi Sunusi Yusuf kan zargin yin fashi ga abokinsa.

Yusuf ya hada baki da wasu inda su ka yi wa wani dan kasuwa Nura Ibrahim fashin kudade har Naira miliyan 2.9 a Kano.

'Yan sanda sun cafke wasu kan zargin yin fashi ga abokin kasuwancinsu a Kano
Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama 'Yan Fashi da Makami A Kano. Hoto: NPF Kano.
Asali: Facebook

Meye ake zargin matasan da aikatawa a Kano?

Sauran wadanda ake zargin wanda tuni an kama su, sun hada da Sunusi Abubakar da Nasiru Ibrahim, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a jiya Laraba 11 ga watan Oktoba a Kano.

Kiyawa ya tabbatar da cewa wandanda ake zargin sun yi wa Nura fashin ne yayin da ya ke tafiya wurin kasuwancinsa a ranar 6 ga watan Oktoba.

Ya ce Yusuf ne a matsayin abokin wanda aka yi wa fashin ya tabbatar musu cewa Nura ya na tare da kudade a jikinsa, Akahi News ta tattaro.

Kiyawa ya ce:

"A ranar 6 ga watan Oktoba, mun samu rahoton fashi daga Nura Ibrahim da ke kauyen Kankiya a karamar hukumar Garko yayin da ya ke tafiya Kaduna don kasuwanci.
"An kai masa farmaki inda aka ji masa raunuka tare da kwace masa makudan kudade har Naira miliyan 2.9."

Wane mataki aka dauka kan matasan a Kano?

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekaru 19 Da Ya Binne Kaninsa Da Rai a Wata Jihar Arewa

Kakakin ya ce bayan samun rahoton ne jami'ansu su ka isa wurin tare da daukar Nura zuwa asibitin Garko don ba shi kulawa.

Ya ce daga bisani an kama Yusuf mai shekaru 25 wanda aboki ne ga Nura da su ke harkar kasuwanci tare.

Har ila yau, an samu muggan makamai a tare da su da kuma Naira dubu 611 inda Kiyawa ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

'Yan sanda sun cafke mata da zargin kashe 'yar kishiyarta

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wata mata kan zargin kisan kai.

Matar mai suna Khadija Adamu ta hallaka 'yar kishiyarta ce bayan ta yi kashi a jikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel