Ana Batun 2027, Gwamna Sule Ya Tono Sirrrin APC kan Nasarar da Ta ke Samu

Ana Batun 2027, Gwamna Sule Ya Tono Sirrrin APC kan Nasarar da Ta ke Samu

  • Gwamna Abdullahi Sule ya ce APC ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa saboda tana samun karbuwa
  • Abdullahi Sule ya tarin ƙuri'un da jam'iyyar APC ta samu a zaben cike gurbin da aka yi a Nasarawa ya nuna irin karɓuwar jam'iyyar a jihar
  • Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar APC, Danladi Envulu-Anza, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 45,362

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jam'iyyar ta samu gagarumar nasara a zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa.

Ya ce sun yi nasara ne saboda al'ummar jihar suna ganin tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Takarar Atiku Abubakar 'tana ƙasa tana dabo'

Abdullahi Sule a wajen taro
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya fadi haka ne da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin sake gina babbar hanyar Akwanga zuwa Jos a Gwanje da ke ƙaramar hukumar Akwanga.

'APC ta samu karbuwa,' Sule

Gwamnan ya ce jam'iyyun adawa sun tsayar da fitattun 'yan takara masu ƙarfi, amma APC ta samu ƙuri'u 45,000, yayin da jam'iyya ta biyu ta samu ƙuri'u 12,000, sannan ta uku ta samu ƙuri'u 11,000.

Ya ce ko da aka haɗa ƙuri'un manyan jam'iyyun adawar biyu, ba su kai rabin abin da APC ta samu ba, wanda hakan ya nuna ta tsere su sosai.

Sule ya jaddada cewa wannan gagarumar nasara ba ta samu ne bisa sa'a ko wata dabara ba, illa saboda ayyukan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin APC a Nasarawa suke yi, waɗanda ya ce jama'a suna yabawa.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa zaɓen ya kasance gwaji ne kafin babban zaɓen shekarar 2027, inda ya ce sakamakon ya tabbatar da cewa APC na ci gaba da samun karɓuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan takara 26 da APC ta sauya sunayensu bayan zaben fitar da gwani

Yadda APC ta yi nasara

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Danladi Envulu-Anza na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa an gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin da rasuwar tsohon Sanatan yankin, Godiya Akwashiki, ta haifar.

Gwamnan Nasarawa tare da 'yan APC
Gwamna Abdullahi Sule a wajen taron APC. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Jami'in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Aminu Ali, ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamako da ke Kwalejin Ilimi ta Akwanga, inda ya bayyana cewa Envulu-Anza ya samu ƙuri'u 45,362, tare da kayar da sauran 'yan takara biyar.

Kiran Gwana Sule kan almajirai

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bukaci gwamnatin Najeriya ta haramta almajiranci.

Ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana kan rashin tsaro da lalacewar ilimi, inda ya ce almajiranci na cikin abin da ke kara ruruta matsalolin.

Abdullahi Sule ya bukaci gwamnonin Arewa su hada kai su dauki matakin da ya dace domin tunkarar matsalolin yankinsu da gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng