Matar Aure Ta Yi Ajalin ’Yar Kishiyarta Saboda Ta Bata Jikinta da Kashi a Jihar Bauchi

Matar Aure Ta Yi Ajalin ’Yar Kishiyarta Saboda Ta Bata Jikinta da Kashi a Jihar Bauchi

  • ‘Yan sanda sun cafke matar aure da ta kashe ‘yar kishiyarta a jihar Bauchi bayan ta bata jikinta da kashi
  • Wacce ake zargin mai suna Khadija Adamu ‘yar shekaru 18 ta yi wa ‘yar kishiyar ta ne duka mai shekaru biyar
  • Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Auwal Musa Muhammad shi ya tabbatar da haka inda ya ce su na kan bincike

Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta cafke matar aure a jihar kan zargin kashe ‘yar kishiyarta saboda ta bata jikinta da kashi.

Wacce ake ake zargin, Khadija Adamu mai shekaru 18 ta yi ta dukan ‘yar kishiyar tata ce mai shekaru biyar a yankin Kandahar da ke cikin Bauchi.

Matar aure ta hallaka 'yar kishiyarta saboda ta yi kashi a jikinta
Jami'an 'yan sanda sun kama matar aure a jihar Bauchi. Hoto: NPF Bauchi.
Asali: Facebook

Meye matar ta aikata a jihar Bauchi?

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Auwal Musa Muhammad shi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kawo rahoton faruwar lamarin ne a ranar 28 ga watan Satumba na 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Watanni 4 An Samu ‘Dan Majalisar Farko da Ya Rasu a Majalisar Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bayan samun rahoton, an fara binciken lamarin babu bata lokaci inda aka yi nasarar kama matar tare da daukar yarinyar zuwa asibiti don ba ta kulawa.

Daga bisani bayan kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, likitoci sun tabbatar da mutuwar yarinyar nan take, Daily Trust ta tattaro.

Kwamishinan ya ce:

“A ranar 28 ga watan Satumba na 2023, wani mai suna Abdul’azizi Adamu mai shekaru 35 da ke Unguwar Kandahar ya kawo rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda da misalin karfe 9:25 na dare.
“Rahoton na cewa wata mata mai shekaru 18, Khadija Adamu a Kandahar ta daka Hafsat Garba mai shekaru biyar wacce ‘yar kishiyarta ce wanda har ya jawo mata raunuka a jiki.”

Meye matar ke cewa kan abin da ta aikata a Bauchi?

Kara karanta wannan

'Yan Bindga 67 Sun Baƙunci Lahira Yayin da Jami'ai Suka Ceto Mutane 20 da Aka Yi Garkuwa da Su a Bauchi

Kwamishinan ya kara da cewa binciken da aka gudanar na farko ya tabbatar cewa matar da yi wa yarinyar dukan tsiya saboda yin kashi a jikinta, cewar Tribune.

Ya ce hakan ya jawo ta samu raunuka a jikinta yayin da wacce ake zargin ta tabbatar da faruwar hakan ba tare da bata lokaci ba.

A martaninta, Khadija Adamu ta ce:

“Na yi amfani da wayar caji na waya saboda ta bata jikinta da kashi wanda ni na yi hakan ne ba don na kashe ta ba duk da cewa ta saba yin hakan a jikinta.
“Na yi dana sanin aikata haka, ina neman afuwa saboda mahaifiyar yarinyar da kuma mahaifinta duk sun yafemin.
“Ina bukatar hukumomi su yafemin saboda cikin da na ke dauke da shi a halin yanzu.”

'Yansa sun yi martani kan matar da aka kama da harsasai

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta yi martani kan matar da aka kama da harsasai a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP Ta Tura Muhimmin Sako Ga Mansur Sokoto, Ta Bayyana Matsayar Ta Kan Kalamansa

Matar an kama ta ne da jaka wanda ke cike da harsasai daga jihar Bauchi zuwa Katsina a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel