Fusatattun Matasa Sun Far Ma Wani Dan Achaba kan Satar Mazakuta a Abuja

Fusatattun Matasa Sun Far Ma Wani Dan Achaba kan Satar Mazakuta a Abuja

  • Wani abun bakin ciki ya afku a yankin Nyanya da ke Abuja bayan fusatattun matasa sun far ma wani dan achaba mai suna Yahuza har lahira
  • An rahoto cewa wasu fusatattun matasa sun farmaki marigayin bayan fasinjarsa ya koka cewa bai ga mazakuatrsa ba
  • An tattaro cewa jami'an tsaro sun isa wajen bayan an dauki dan keken zuwa asibiti inda ya mutu

Abuja, Nyanya - Wasu fusatattun matasa sun farmaki wani dan achaba mai suna Yahusa, kan zargin sace mazakutar fasinjansa a yankin Nyanya da ke Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wani ganau mai suna Ibrahim Musa, ya ce mummunan al'amarin ya afku ne da misalin karfe 5:12 na yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

Matasa sun halaka wani kan zargin sace mazakuta
Fusatattun Matasa Sun Far Ma Wani Dan Keke kan Satar Mazakuta a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Musa ya yi bayanin cewa dan acahaban ya dauki fasinja daga 'Old Karu' zuwa Nyanya amma jim kadan bayan fasinjan ya sauka daga achaban sai ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba.

Kara karanta wannan

Makaho Mai Maganin Gargajiya Ya Damfari Dattijuwa Miliyan 19, Ya Kuma Kwanta Da 'Yarta Da Jikarta

Wani ganau ya ce kokawar da ya yi ya ja hankalin wasu mutane, wadanda suka far ma dan achaban da sanduna da muggan makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar daga bisani wasu masu wucewa sun ceci dan achaban sannan suka dauke shi zuwa asibiti mafi kusa.

Musa ya ci gaba da cewa an dauki dauki shima fasinjan zuwa wani asibiti a Nyanya don tabbatar da ikirarinsa na rasa mazakutarsa.

"Abun takaici, dan achaban ya rasu daga bisani a asibitin da aka kai shi kafin jami'an tsaro su isa wajen."

Ihun batan mazakuta duk karya ce

Kakakin yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ya ce dukkan batutuwan batan mazakuta duk karya ce.

Adeh ta bayyana cewa an kai mutane da dama kotu kan irin wadannan zarge-zargen.

Kakakin yan sandan ta ce:

"Kwamishinan yan sandan ya bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton irin wannan lamarin ofishin yan sanda domin laifi ne daukar doka a hannu; wadanda aka kama da hannu a lamarin za su fuskanci mataki na doka."

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Zargin Satar Mazakuta A Abuja, Ya Ba Da Shawara

Shehu Sani ya yi Allah wadai da ma su daukar mataki kan zargin satar mazakuta a Abuja

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da masu daukar doka a hannunsu kan wadanda ake zargi da satar mazakuta.

Sani na magana ne musamman a birnin Tarayya Abuja da abin yanzu ya yi kamari, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel