ICPC Sun Cafke Tsohon Ministan Tinubu Mai Takarar Gwamna a Filin Jirgin Sama
- An kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya na Abuja
- Majiyoyi sun ce za a mika shi ga hukumar ICPC domin yi masa tambayoyi kan zargin amfani da takardun karatun bogi
- Majiyoyi sun ce Nnaji ya gabatar da takardun bogi ga gwamnatin tarayya, yayin da kotu ta ba ICPC umarnin kama shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, ya higa hannun jam'ian hukumar yaki da cin hanci ta ICPC.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama shi a ranar Laraba 1 ga watan Yulin 2026 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Source: Twitter
Rahoton Premium Times ya tabbatar da cewa an kama Nnaji ne bayan dawowarsa daga Enugu ta jirgin haya.
Majiyoyi masu tushe a filin jirgin sun tabbatar cewa an kama Mista Uche Nnaji, sannan za a mika shi ga Hukumar ICPC domin yi masa tambayoyi.
ICPC ta dade tana farautar Uche Nnaji
Hukumar ICPC ta dade tana neman tsohon ministan tun bayan murabus dinsa a bara, bincike ya nuna ana zarginsa da ƙirƙirar takardun shaidar karatunsa na bogi.
A tsakiyar watan Yuni, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci ICPC ta kama Uche Nnaji, kotun ta kuma ba hukumar izinin ayyana shi a matsayin wanda ake nema.
Hukumar ICPC ta shaida wa kotun cewa ta nemi wannan umarni ne saboda Mista Nnaji ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa sau da dama.
Gayyatar ICPC ta biyo bayan binciken shekaru biyu da aka yi wanda ya bayyana cewa tsohon ministan ya ƙirƙira takardar digirinsa ta Jami'ar Najeriya, Nsukka da takardar NYSC.

Source: Twitter
Yadda Nnaji ya gabatar da takardun ga Tinubu
Rahoton ya ce ya gabatar da takardun bogin ga Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa yayin tantance ministoci a shekarar 2023 domin samun amincewa.

Kara karanta wannan
Akwai dalili: Gwamnatin tarayya za ta rushe tsarin karatun sakandare na JSS da SSS
Binciken ya kuma nuna cewa an gabatar da takardun ga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Hukumar DSS da kuma Majalisar Dattawa a lokacin tantancewar.
Daga baya tsohon ministan ya amince cewa Jami'ar Najeriya, Nsukka ba ta ba shi takardar digiri ba, cewar Punch.
Da farko Mista Nnaji ya musanta cewa akwai umarnin kotu na kama shi bayan yada hakan a kafafen yada labarai.
A ranar 18 ga Yunin 2026, Mista Nnaji ya daukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ya nemi a soke umarnin kama shi da kotun ta bayar.
Tsohon minista ya samu tikitin takarar gwamna
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ya samu nasara a zaben fitar da 'dan takarar gwanna na jam'iyyar PDP a jihar Enugu.
Tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya tabbatar da Nnaji a matsayin dan takarar gwamnan a karkashin inuwar PDP a zaben 2027.
Dan siyasar dai ya rasa kujerarsa ta minista ne sakamakon zargin da ake masa na amfani da takardun digiri da na NYSC na bogi.
Asali: Legit.ng
