Allah Ya Ceci Wani Mutumi da Matarsa Ta Lallaba Za Ta Yanka Masa Wuya Yana Barci a Katsina

Allah Ya Ceci Wani Mutumi da Matarsa Ta Lallaba Za Ta Yanka Masa Wuya Yana Barci a Katsina

  • Wata matar aure yar kimanin shekara 23, Sadiya Lawal ta yi yunkurin kashe mijinta ta hanyar yanka masa wuya yana cikin barci a jihar Katsina
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun kama matar
  • Magidancin ya bada labarin yadda matarsa da farmake shi yana barci, yanzu haka kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - An shiga tashin hankali a cikin birnin jihar Katsina bayan wata matar aure 'yar kimanin shekara 23 ta yi yunkurin kashe mijinta yana cikin barci a gidansa.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta daba wa mijinta wuƙa a wuya a yayin da yake barci, lamarin da ya jikkata shi amma bai mutu ba har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Zafi ya shiga Turai yana ta kashe mutane a Faransa da sauran kasashe

Yan sanda.
Jami'an hukumar 'yan sanda ta Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Leadeship ta rahoto cewa mutumin, mai suna Jamilu Ibrahim, ya tsira daga harin kuma yana samun kulawa a asibiti, yayin da Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta kama matarsa, Sadiya Lawal.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2026.

Yadda mata ta kusa kashe mijinta

A cewar rundunar 'yan sanda, Jamilu Ibrahim ya kai rahoton abin da ya auku ofishin 'yan sanda na Central Market da misalin ƙarfe 9:00 na safe

A rahoton da ya shigar a wurin 'yan sanda, magidancin ya ce matarsa ta kai masa hari da misalin ƙarfe 5:30 na asubahi yayin da yake barci.

Rahoton ya ce matar ta yi ƙoƙarin yanke masa wuya da wata kaifaffiyar wuƙa, amma ba ta samu nasara ba.

'Yan sanda sun ce mijin ya samu mummunan rauni a wuya, inda aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa domin ba shi kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza

Bayanai daga asibitin sun bayyana cewa Jamilu Lawal yana ci gaba da amsar magani kuma yana samun sauki.

Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun kama matar a Katsina

Bayan samun rahoton, jami'an sashen bincike na rundunar yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru, inda suka kama matar tare da ƙwace wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen yunkurin kisan kai.

Rundunar ta ce matar na tsare a hannunta yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala bincike, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Amarya ta yanka ango har lahira a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa ana zargin wata amarya da ba a dade da daura aurenta ba, mai suna Fatima da kashe angonta, Auwalu a unguwar Rimin Kebe ta jihar Kano.

Ganau da lamarin ya auku a kan idonsu sun ce matar ta yanka makogwaron angonta yayin da sabani ya shiga tsakaninsu.

Dakarun rundunar ’yan sanda sun garzaya wurin bayan samun rahoto, kuma an ce sun kama matar da ake zargi domin ci gaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262