ICPC Ta Samu Damar Yin Yadda Ta So da Tsohon Ministan Tinubu da Aka Kama
- Uche Nnaji wanda ya rike Ministan kirkira, kimiyya da fasa a farkon mulkin Bola Ahmed Tinubu yana cikin ragar ICPC
- Jami’an DSS suka cafke shi kuma suka mika shi wajen masu neman shi, kuma da alama yanzu ya fara zama a hannun nasu
- Hukumar ICPC ta ke kotu ta nemi izinin cigaba da rike Nnaji na makonni biyu domin yi masa tambayoyi na bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar ICPC mai yaki da rashin gaskiya ta samu damar cigaba da rike Uche Nnaji, tsohon Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya.
Bayan cafke shi da ta yi a makon nan, yanzu jami’an hukumar suna da hurumin rike Uche Nnaji da sunan bincike har a kai ga gurfanar da shi a kotu.

Source: Facebook
Hukumar ICPC ta samu izinin rike Uche Nnaji
Wani jami’i na hukumar ICPC ya shaida wa Premium Times cewa sun samu takardar kotu da ta ba su izinin cigaba da rike tsohon ministan kasar.

Kara karanta wannan
An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi
A dalilin haka, Uche Nnaji zai iya shafe kwanaki akalla 14 saboda takardar da kotu ta ba ICPC. Idan akwai bukata, za a iya neman karin kwanaki.
Wannan izini da kotu ta ba jami'an ICPC za su hana Nnaji ya zargi hukumar da keta masa alfarma ko da sun rike shi na fiye da kwanakin da aka halatta.
Yadda aka kama Uche Nnaji a filin jirgi
An kama tsohon ministan ne a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja, hakan ta faru ne jim kadan bayan ya dawo daga jihar Enugu.
Jami’an da suka kama shi a jirgin sun yi maza-maza suka damka shi hannun hukumar ICPC.
Kakakin ICPC na kasa, John Ode tya tabbatar da cewa Nnaji wanda yanzu yake neman takarar gwamnan jihar Enugu a inuwar PDP ya shigo hannu.
Tun a watan Oktoban 2026 ake neman Nnaji ya amsa wasu tambayoyi, amma ya gagara bayyana gaban hukumar ICPC domin ya iya wanke kan shi.
Su kuma ICPC sun bukaci su zauna da shi ne sanadiyyar rahotanni da ita wancan jarida ta fitar bayan shafe shekaru sama da biyu ana bincike game da shi.
An kama shi ne da taimakon jami’an DSS sai aka damka shi ga ICPC domin cigaba da bincike.
A sakamakon kama shi, an dauke Nnaji zuwa wani wuri a hedikwatar ICPC in Abuja, inda ake sa ran cigaba da bincike da nufin gano gaskiyar zargin da ake yi.
ICPC za ta yi wa tsohon ministan tambayoyi
Rahoton PM News ya ce hukumar ta sanar cwa za a binciki lamarin da kyau yadda doka ta tanada, hakan zai toshe zargin keta hakkin wanda ake tuhuma.
John Odey ya yi karin bayani cewa sun samu izini daga kotu ganin yadda ‘dan siyasar ya rika watsi da gayyatar da ICPC ta yi ta aika masa a can baya.
Ban da zargin yana amfani da takardar digirin bogi, kakakin ICPC ya kara da cewa ana zargin Nnaji da yin karya game da batun kammala bautar NYSC.
Akwai zargin cewa ‘dan siyasar ya mika takardar kammala bautar kasa wato NYSC na bogi lokacin da aka nemi takardunsa, a nada shi minista a 2023.
Masu binciken za su iya daukar kwanaki 14 suna yi masa tambayoyi, idan kuma bukata ta tashi, hukumar ICPC za ta iya neman alkali ya kara lokaci.
'Yan sanda sun cafke kakakin jam'iyyar PDP
Mai magana da yawun jam'iyyar PDP ya shiga hannu a sakamakon zargin cin mutuncin tsohon sanata a Akwa Ibom kamar yadda aka samu labari kafin yanzu.
Kakakin PDP ya fada hannun ‘yan sanda kuma jami’ai sun bayyana cewa abin da ya aikata laifi ne da zai jawo a gurfanar da shi a kotu idan ta kama.
Duk da PDP NWC ta soki aikin 'yan sandan, sai dai an ji cewa Mista Ewa Okpo ya yi wasu maganganu da suka jawo masa matsala da Sanata Effiong Bob.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

